Mutuwar Sanata Ta Dakatar da Zaman Majalisar Tarayya, Bayanai Sun Fito
- Majalisar wakilai ta ɗage zamanta na farko bayan dawowa daga hutun shekara-shekara domin jimami da karrama marigayi Sanata Ifeanyi Ubah
- Sanatan mai wakiltar Anambra ta Kudu a majalksar dattawa ya riga mu gidan gaskiya ne a watan Yuli lokacin ƴan majalisa sun tafi hutu
- Kamar yadda al'adar majalisar tarayya ta tanada, idan ɗan majalisa ya rasu, a kan ɗage zaman ranar farko, an sanar da sai Laraba za a dawo zama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar wakilai ta tarayya ta ɗage zamanta na yau Talata, 24 ga watan Satumba, 2024 domin karrama marigayi Sanata Ifeanyi Uba.
A yau majalisar ta ke dawowa daga hutun shekara-shekara wanda kundin tsarin mulki ya tanada, to sai dai ta ɗage zamata zuwa gobe Laraba domin girmama marigayin.
Sanata Ubah ya rasu a Landan
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Sanata Ubah mai wakiltar Anambra ta Kudu ya mutu ne ranar 27 ga watan Yuli, 2024 a lokacin majalisar ta tafi hutu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan matakin da majalisar wakilai ta dauka ya yi daidai da al’adar majalisar dokokin Najeriya na dakatar da zaman farko idan wani ɗan majalisa ya kwanta dama.
Bayanai sun nuna Sanata Ifeanyi Ubah ya riga mu gidan gaskiya ne bayan ya tafi ƙasar Burtaniya domin a yi masa tiyata.
Ya rasu ne mako ɗaya gabanin ranar 3 ga watan Satumba, 2024, ranar da zai cika shekara 53 a duniya, cewar rahoton Vanguard.
Majalisa ta ɗage zama domin karrama Sanata Ubah
Rasuwar sanatan na jam'iyyar APC ta jefa ƴan Najeriya musamman abokansa na siyasa cikin jimami da alhini.
A halin yanzu dai majalisar wakilai ta ƙasa ta sanar da ɗage zamanta na farko daga yau Talata zuwa gobe Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024 domin girmama shi.
Majalisar dattawa ta tallafawa Maiduguri
A wani rahoton kuma Majalisar dattawan kasar nan ta aika tawaga ta musamman zuwa Borno domin jajanta wa gwamna Babagana Zulum kan ambaliya.
Jama'a sun shiga cikin mawuyacin hali bayan ruwa ya haura madatsar Alau, ya kuma mamaye gidaje, hanyoyi da sauran wurare a babban birnin jihar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng