Shugaban Yarabawa Ya Bukaci a Raba Najeriya, Ya Turawa Gwamnoni, Sarakuna Sako

Shugaban Yarabawa Ya Bukaci a Raba Najeriya, Ya Turawa Gwamnoni, Sarakuna Sako

  • Shugaban kungiyar Yarabawa ta YSM, Farfesa Banji Akintoye ya yi magana kan buƙatar raba Najeriya da ba Yarabawa yanci
  • Farfesan ya kuma yi kira ga gwamnonin Kudu maso Yammacin Najeriya kan ayyana ranar Yarabawa ta kasa a jihohinsu
  • Shugaban Yarabawan ya fadi abubuwan da suka sanya shi yin kira domin raba Najeriya a daidai irin wannan lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Wani shugaban kungiyar Yarabawa, Farfesa Banji Akintoye ya bukaci a ba Yarabawa kasarsu a Najeriya.

Farfesa Banji Akintoye ya ce ana cutar da Yarabawa sosai kasar nan kuma hanyar ware musu kasa ce kawai sauki a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya rarrashi yan Najeriya, ya yi alkawarin samun saukin rayuwa

Banji
Farfesa Banji ya bukaci raba Najeriya. Hoto: @Smartdon1996
Asali: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa Farfesa Banji Akintoye ya yi kira na musamman ga sarakuna da gwamnonin Kudu maso Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Yarabawa ya ce a raba Najeriya

Shugaban kungiyar Yarabawa ta YSM, Farfesa Banji Akintoye ya bukaci gwamnati ta ware Yarabawa a Najeriya.

The Nation ta wallafa cewa Farfesa Banji ya ce hakan ne zai samar da mafita kan yawan kashe musu mutane da makiyaya ke yi a jihohinsu a Najeriya.

Farfesan ya ce idan suka ware kasarsu za su samu kariya da inganta tsaro da kuma haɓaka tattalin arzikin kasar Yarabawa.

Maganar hadin kan Yarabawa

Farfesa Banji Akintoye ya yi kira ga gwamnoni da sarakunan Kudu maso Yammacin Najeriya da su samar da ranar Yarabawa a kasarsu.

Ya ce idan aka ayyana ranar ya kamata a mayar da ita hutu na musamman a dukkan garuruwan Yarabawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga taron FEC ana rade raɗin za a kori wasu ministoci, bayanai sun fito

Saboda haka Farfesa Banji ya ce idan gwamnonin suka hadu ya kamata su yanke matsaya kan samar da ranar Yarabawa domin haɗin kai.

Wasu Yarabawa sun bukaci raba Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ta da kayar baya ta Yarabawa masu neman ficewa daga Najeriya sun bukaci a raba ƙasar cikin watanni biyu.

Wannan kungiyar ta fitar da sanarwar ce a wata budaddiyar wasika da ta rubuta wa fadar shugaban kasa inda ta bayyana dalilan yin kiran.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng