“Yarintarmu Na Ke Tunawa”: Tinubu Ya Kadu da Mutuwar Yayansa Mai Shekaru 80

“Yarintarmu Na Ke Tunawa”: Tinubu Ya Kadu da Mutuwar Yayansa Mai Shekaru 80

  • EhAn sanar da rasuwar yayan Shugaba Bola Tinubu mai suna Dakta Naheemdeen Ade Ekemode wanda ya kasance dan baffansa
  • Marigayin ya kasance dan uwan Tinubu da ya ba da gudunmawa mai tsoka ta musamman a harkokin lafiya saboda kasancewarsa likita
  • Tinubu ya bayyana irin shakuwar da suka yi tun suna yara da kuma girmansu inda ya yi masa addu'ar samun rahamar Ubangiji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziyya bayan mutuwar dan uwansa, Dakta Naheemdeen Ade Ekemode.

Marigayin ya kasance yayan Shugaba Tinubu wanda ya rasu a jiya Litinin 23 ga watan Satumbar 2024 yana da shekaru 80.

Kara karanta wannan

Dorinar Ruwa ta yi ajalin dogarin Sarki, Gwamna ya kadu

Tinubu ya kadu bayan rasuwar yayansa mai shekaru 80
Bola Tinubu ya yi alhinin rashin yayansa. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

Tinubu ya yi jimamin rasuwar yayansa, Naheemdeen

Hadimin Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Tinubu ya tuno lokacin yarintarsu inda ya yabawa marigayin kan gudunmawar da ya bayar a harkar lafiya.

Tinubu ya godewa marigayin game da lokutan da suka kwashe tare tun daga yarinta har zuwa girmansu inda ya fadi abubuwan da ya koya a lokacin zamansu.

Ya bayyana irin gibi da marigayin ya bari bayan mutuwarsa sai dai ya yi imanin cewa Ekemode na cikn amince da natsuwa.

Tinubu ya jajantawa iyalan Dakta Naheemdeen Ekemode

Har ila yau, Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin inda ya yi addu'ar samun rahama gare shi da kuma hakuri ga iyalansa.

Shugaba Tinubu ya yabawa marigayin game da gudunmawar da ya bayar wurin taimakon al'umma ta bangaren lafiya.

Kara karanta wannan

Wata tanka maƙare da man fetur ta fashe, ta yi wa mutane illa a birnin Abuja

Ya ce sadaukarwarsa ba za ta tafi a banza musamman wadanda ya warkar yayin da shafe shekaru 50 yana bautawa al'umma.

Hadimin gwamnan Katsina ya rasu

Mun ba ku labarin cewa hadimin gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda a bangaren harkokin matasa ya riga mu gidan gaskiya.

An tabbatar da rasuwar marigayin mai suna Aminu Lawal Custom a ranar Alhamis 19 ga watan Satumbar 2024.

Kafin rasuwar marigayin, yana daga cikin masu neman takarar shugaban karamar hukumar Malumfashi da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.