Rahoton Yiaga Ya Zargi INEC da Tafka Maguɗi a Zaben Edo, Bayanai Sun Fito

Rahoton Yiaga Ya Zargi INEC da Tafka Maguɗi a Zaben Edo, Bayanai Sun Fito

  • Kungiyoyin sa-kai masu lura da yadda zaben gwamnan jihar Edo ya gudana a ranar Asabar sun fara fitar da rahoton bayan zabe
  • Kungiyar Yiaga Africa ta fitar da rahoto kan yadda zaben ya gudana da kuma kurakurai da ta ce an tafka a ɓangaren hukumar INEC
  • A ranar Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa dan takarar APC, Monday Okpebholo ne ya lashe zaben Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - An fara samun bayanai kan yadda zaben gwamnan jihar Edo ya gudana a ranar Asabar da ta wuce.

Kungiyar Yiaga Africa, wacce na cikin kungiyoyin da suka saka ido kan zaben ta fitar da rahoto kan yadda zaben ya gudana.

Kara karanta wannan

'An yi kwacen mulki a Edo,' Gwamna ya yi zazzafan martani kan zabe

Zaben Edo
Yiaga ta yi zargin magudi a zaben Edo. Hoto Asue Ighodalo|Monday Okpebholo|Akpata Olumide Anthony
Asali: Twitter

Legit ta gano rahoton da Yiaga Africa ta fitar ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X a yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yiaga Africa ta saka ido a zaben Edo

Kungiyar Yiaga Africa ta ce ta saka ido a zaben Edo a kan yadda ya gudana a dukkan kananan hukumomin jihar 18.

Haka zalika kungiyar ta ce ta saka ido kan yadda aka tattara sakamakon zabe a dukkan kananan hukumomin da hedikwatar INEC da ke Benin.

Yiaga ta ce zaben Edo ba sahihi ba ne

Kungiyar Yiaga ta ce an samu canje canjen sakamakon zabe a wasu mazabu a wasu kananan hukumomin jihar.

Bayan haka, ta ce an yiwa wasu jami'an INEC da na jam'iyyu barazana wanda hakan yasa zaben bai zama ingantacce ba.

Yiaga ta ce jami'an INEC su yi maguɗi

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar rikici a Edo: 'Yan sanda sun dauki matakai bayan nasarar APC

Daily Trust ta wallafa cewa rahoton Yiaga Africa ya nuna cewa an samu rashin daidaito kan yadda sakamako suka fito daga ƙananan hukumomin Edo.

A karkashin haka, Yiaga Africa ta yi zargin cewa wasu jami'an INEC sun yi aringizon kuri'u kuma an samu katsalandan din wasu jami'an tsaro.

Yiaga ta yi kira kan gyara harkar zabe

Kungiyar Yaiaga Africa ta ce akwai bukata mai matukar muhimmanci kan kawo gyara a harkar zabe a Najeriya.

Yaiaga ta kuma yi kira ga yan siyasar Najeriya kan cewa ya zama wajibi su canza hali musamman a kan abin da ya shafi zabe.

Gwamna ya koka kan zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya nuna takaici kan yadda hukumar INEC ta sanar da cewa APC ta lashe zaben gwamna.

Godwin Obaseki ya yi kira na musamman ga al'ummar jihar Edo kan cigaba da rungumar zaman lafiya duk da abin da ya faru a Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng