Zance Ya Kare: Kotu Ta Yanke Hukunci kan Bukatar Tsige Ganduje daga Shugaban APC
- A yanzu Abdullahi Ganduje ya san matsayinsa a shugabancin jam'iyyar APC na kasa bayan da wata babbar kotun tarayya ta yi hukunci
- Babbar kotun bisa jagorancin Mai shari'a Inyang Ekwo ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta na neman a tsige Abdullahi Ganduje
- Mai shari'a Ekwo ya ce nada shugabannin APC wani al'amari ne na harkokin jam'iyyar wanda babu wata kotu da za ta tsoma baki a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci kan bukatar da aka gabatar a gabanta na tsige Abdullahi Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC.
Kotun ta kori karar da aka shigar a gabanta, inda ta jaddada cewa Ganduje zai ci gaba da zama a matsayin shugaban APC na kasa.
APC: Kotu ta ki tsige Ganduje
Jaridar The Nation ta rahoto kotun ta yanke hukuncin ne a safiyar ranar Litinin, inda Mai shari’a Inyang Ekwo ya sallami karar wadda wata kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ta shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Inyang Ekwo yanken hukuncin cewa babu hujjoji a karar kuma shari'ar ta shafi wani al'amari na harkokin kasa da kasa na jam'iyyar siyasa.
Mai shari’a Ekwo ya kuma bayyana cewa kungiyar da ta shigar da karar ba ta da hurumi kasancewar ba a yi mata rajista a shari’a ba.
Alkali ya ba da dalilin hukunci
Alkalin ya ce wannan kadai ya isa ya sa a kori karar kasancewar kungiyar ba ta da wani hurumi na shigar da wannan karar a shari'ance.
Kotun ta kuma kara da cewa kungiyar APC ta Arewa ta gaza amfani da dabarun warware rikicin shugabancin jam'iyyar a cikin lumana kafin tunkarar kotun.
Mai shari’a Ekwo ya ce nadin shugabannin APC da kwamitin zartarwarta na kasa (NEC) ya yi lamari ne na cikin gida na jam’iyyar wanda babu wata kotu da za ta iya shiga cikinsa.
Tsige Ganduje: Kotu ta dauki mataki
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke a jihar Kano ta dakatar da jam'iyyar APC daga korar shugabanta na kasa, Abdullahi Ganduje.
An shigar da karar gaban kotun inda ya kalubalanci matakin APC reshen gundumarsa na korarsa daga jam'iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng