Zaben Edo: INEC Ta Fara Tattara Sakamakon Zabe, Bayanai Sun Fito

Zaben Edo: INEC Ta Fara Tattara Sakamakon Zabe, Bayanai Sun Fito

  • Daga ƙarshe hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo
  • Hukumar zaɓen ta fara tattara sakamakon ne biyo bayan ta kasa fara ci gaba da aikin tattara sakamakon zaɓen da safiyar ranar Lahadi
  • Ƴan takarar APC da PDP ne ke kan gaba wajen samun mafi yawan ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo.

Hukumar ta fara tattara sakamakon zaɓen ne bayan ta wuce lokacin da tun da farko ta ce za ta fara aikin.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Dan takarar PDP ya fara karaya, ya zargi hukumar INEC

INEC ta fara tattara sakamakon zaben Edo
INEC na tattara sakamakon zaben gwamnan Edo Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

INEC ta fara tattara sakamakon zaɓen Edo

Jaridar Daily Trust ta ce jagororin tattara sakamakon zaɓen duk sun zauna a harabar ɗakin da ake gudanar da aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikinsu akwai kwamishinan INEC na ƙasa mai kula da zaɓen, Rhoda Gumus, kwamishinan INEC na jihar Edo Dr. Anugbum Omuoha, da baturen zaɓen jihar Farfesa Faruk Adams Kuta.

Da yake jawabi wajen buɗe aikin tattara sakamakon zaɓen, Anugbum Omuoha ya sha alwashin cewa hukumar ba za ta ba al'ummar jihar Edo kunya ba yayin da ake ci gaba da gudanar da zaɓen gwamnan.

Ya bayyana cewa daga ƙarshe mutane za su samu abin da suka zaɓa, inda ya yi kira ga mutane da su ci gaba kwantar da hankulansu.

INEC ta faɗi lokacin tattara sakamako

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da lokacin da za ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo.

Kara karanta wannan

IREV: Ana daf da kammala daura kuri'un zaben Edo, an kusa sanin sabon gwamna

Hukumar INEC ta bayyana cewa za ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:00 na safe a ranar Lahadi.

Kwamishinan zaɓen ya tabbatarwa jama’a cewa za a gudanar da aikin tattara sakamakon zaɓen cikin gaskiya, daidai da ƙa’idojin hukumar

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng