Zaben Edo: PDP, APC Na Zaman Ɗari Ɗari Bayan INEC Ta Gaza Fara Tattara Sakamako
- Ya zuwa wannan lokaci, an rahoto cewa hukumar INEC ba ta soma tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka yi jiya ba
- Tun da fari, INEC ce da kanta ta sanar da cewa zuwa karfe 10:00 na safiyar yau Lahadi za ta fara tattara sakamakon a ofishinta na Benin
- Sai dai har yanzu babu alamar fara tattara sakamakon, lamarin da aka ce ya haifar da zaman dari dari a fadin jihar ta Edo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Har yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ranar Asabar ba.
Babban ofishin INEC da ke Benin, babban birnin Edo, shi ne cibiyar tattara sakamakon zaben jihar.
Ana dai zaman dari dari a jihar sakamakon tsaikon da aka samu wajen bayyana sakamakon zaben a hukumance, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
INEC ta gaza fara tattara sakamako
Dakta Anugbum Onuoha, baturen zabe na INEC (REC) na jihar Edo, a wata sanarwa da ya fitar ya ce za a fara tattara sakamakon zaben da karfe 10 na safiyar ranar Lahadi.
"Muna sanar da jama'a, masu ruwa da tsaki na siyasa da masu sa ido cewa za a soma tattara sakamakon zaben jihar Edo a yau Lahadi 22 ga Satumba da karfe 10:00 na safe."
- A cewar sanarwar Dakta Anugbum.
To sai dai kuma, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar zabe ta INEC ba ta fara tattara sakamakon zaben jihar na Edo ba.
Duba wasu labarai kan zaben Edo:
INEC ta yi barazanar soke sakamakon zaben da aka dora a IReV
EFCC ta cafke mutane uku da laifin sayen kuri'u a zaben Edo
Edo 2024: 'Yan bindiga sun yi awo gaba da wani akwatin zabe
Dalilin zuwan Obaseki ofishin INEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana dalilin da ya sa ya kai ziyara babban ofishin hukumar INEC da ke Benin City.
Obaseki ya ce ya ziyarci ofishin INEC domin ganawa da baturen zaben jihar bayan da ya samu rahotonni na tsaikon fara tattara sakamako da hana wakilan APC shiga dakin tron hukumar.
Asali: Legit.ng