Zaben Edo: 'Yan Sanda Sun Yi Karin Haske yayin da APC, PDP da LP Ke Neman Nasara
- Mataimakin Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, DIG Frank Mba ya bayyana cewa an samu fitowar masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar Edo
- Frank Mba ya bayyana gamsuwa da matakan tsaro da aka ɗauka, yana mai nuna cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana
- Ƴan takara 17 ne suka fafata a zaɓen na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024 inda jam’iyyun APC, PDP da LP ke kan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Mataimakin Sufeto-Janar na ƴan sanda (DIG) Frank Mba ya bayyana cewa jama’a sun fito domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar Edo.
Frank Mba, wanda ke kula da ayyukan tsaro a zaɓen, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, 21 ga Satumba, 2024.
Me ƴan sanda suka ce kan zaɓen Edo?
DIG Frank Mba ya bayyana cewa tawagarsa ta ziyarci rumfunan zaɓe da dama a faɗin jihar, inda suka lura da ɗumbin masu kaɗa kuri’a da suka fito zaɓen, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, kuma ya bayyana cewa an samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'a a wasu rumfunan zaɓen.
"Mun ziyarci rumfunan zaɓe da dama kuma ya zuwa yanzu, mun ga jama'a sun fito da dama."
- Frank Mba
Frank Mba ya yi magana kan yanayin tsaro
Game da samar da tsaro, DIG Frank Mba a bayyana gamsuwa kan yadda zaɓen ya gudana baki ɗaya, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
"A gare mu babban abin da muka damu da shi, shi ne batun tsaro a lokacin kowane zaɓe, kuma ya zuwa yanzu na gamsu da rahotannin da na ke samu.
- Frank Mba
Mataimakin Sufeto-Janar na ƴan sandan ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa ƴan sanda na magance duk wasu ƙananan matsalolin tsaro da suka taso.
Dan takarar PDP ya magantu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Edo, Asue Ighodalo ya ce shi ne zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaɓen.
Asue Ighodalo ya bayyana hakan ne bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓensa da ke makarantar firamare ta Indinrio a Okaigben Ewohomi cikin ƙaramar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas ta jihar.
Asali: Legit.ng