Zaben Edo: PDP Ta Bukaci IGP Ya Janye Babban Jami'in 'Yan Sanda, Ta Fadi Dalili
- Jam'iyyar PDP ta yi kira ga shugaban ƴan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun da ya janye mataimakinsa na shiyya ta bakwai
- PDP ta zargin cewa AIG Benneth Igwe ya haɗa baki da jam'iyyar APC domin ba ƴan daban jam'iyyar kariya su tayar da hargitsi
- Jam'iyyar ta buƙaci Kayode Egbetokun da ya gaggauta cire shi daga aikin zaɓen domin kaucewa samun rikici a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Jam'iyyar PDP ta yi kira da babban murya ga babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun kan zaɓen gwamnan jihar Edo.
Jam'iyyar PDP ta buƙaci Kayode Egbetokun da ya gaggauta janye mataimakin babban sufeton ƴan sanda (AIG) na shiyya ta bakwai, Benneth Igwe, daga aikin zaɓen Edo domin kaucewa tayar da hargitsi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta sanya a shafinta na X mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Debo Ologunagbo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa PDP ke son IGP ya cire Igwe?
PDP ta buƙaci hakan ne biyo bayan zarge-zargen da ake yi cewa AIG Benneth Igwe ya haɗa baki da APC domin ba ƴan daban APC kariya ta yadda za su farmaki cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.
PDP ta yi zargin cewa AIG ɗin ya yi wani zama da wasu jami'an ƴan sanda domin ganin an aiwatar da wannan shirin.
"Saboda haka jam’iyyarmu ta na kira ga IGP da ya gaggauta kiran AIG zuwa Abuja domin ci gaba da zamansa a Jihar Edo tuni ya janyo fargaba a jihar."
"Dole ne AIG ya fito ya yi magana tare da wanke kansa kan wannan babban zargin da ake yi masa."
"Jam’iyyar PDP ta yabawa matasan jihar Edo bisa taka-tsan-tsan da jajircewar da suka nuna wajen ganin cewa ba a karkatar da abin da jama'a suke so ba a wannan zaɓen."
- Debo Ologunagba
Rigima ta ɓarke a zaɓen Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabuwar rigima ta barke a gundumar Orhionmwon da ke karamar hukumar Orhionmwon ta Edo yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa an dakatar da kada kuri'a a rumfa ta daya a gundumar bayan jami'an INEC sun manta da takardar rubuta sakamakon zabe.
Asali: Legit.ng