Zaben Edo: INEC Ta Yi Magana kan Dora Sakamakon Zabe a Na'urar IReV

Zaben Edo: INEC Ta Yi Magana kan Dora Sakamakon Zabe a Na'urar IReV

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ƙasa (INEC) ta bayyana shirinta kan zaɓen gwamnan jihar Edo na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024
  • Kwamishinan INEC na jihar Edo ya bayyana cewa za a yi amfani da na'urorin BVAS wajen tantance masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen
  • Anugbum Onuoha ya tabbatar da cewa za a ɗora sakamakon zaɓen a kan na'urar IReV idan ba a samu matsalar sabis ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta yi ƙarin haske kan hanyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo.

Hukumar INEC ta bayyana cewa za a tattara sakamakon zaɓen ta hanyar yin amfani da na'urar BVAS.

Kara karanta wannan

"Babu makawa": Jigon APC ya yi hasashen wanda zai lashe zaben gwamnan Edo

INEC za ta dora sakamakon zabe Edo a IReV
INEC ta fadi sharadin dora sakamakon zaben Edo a na'urar IReV Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

INEC za ta ɗora sakamako a IReV

Kwamishinan hukumar INEC na jihar Edo, Anugbum Onuoha ya bayyana hakan yayin tattaunawa da tashar Arise tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan na INEC ya bayyana cewa bayan kammala tattara sakamakon zaɓen za a ɗora a IReV idan har ba a samu matsalar sabis ba.

"Muna da rumfunan zaɓe 4,519 a cikin ƙananan hukumomi 18. Ya zuwa yanzu mun aika da na'urorin BVAS guda 4,622 a ƙananan hukumomin."
"Muna da ragowar guda 660 domin shirin ko ta kwana. Mun horar da jami'an da za su yi aiki da na'urar BVAS kuma sun shirya tsaf."
"BVAS za ta tantance masu kaɗa ƙuri'a domin sanin adadin masu kaɗa ƙuri'a a kowace rumfar zaɓe. Za mu gudanar da zaɓen da za mu yi alfahari da shi."
"Bayan kammala kaɗa ƙuri'a, za a ƙirga yawan ƙuri'un da aka samu sannan za a ɗora su a IReV idan a wajen babu matsalar sabis."

Kara karanta wannan

Zaben Edo: 'Yan sanda sun yi gargadi ana dab da fara kada kuri'a

- Anugbam Onuoha

Zaɓen Edo: Jigon APC ya yi hasashe

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam’iyyar APC, Francis Okoye, ya yi hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan jihar Edo wanda za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumba.

Francis Okoye ya ce babu makawa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo, zai kayar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng