Ighodalo vs Okpebolo: Jigon PDP Ya Hango Wanda Zai Lashe Zaben Gwamnan Edo

Ighodalo vs Okpebolo: Jigon PDP Ya Hango Wanda Zai Lashe Zaben Gwamnan Edo

  • Dare Glintstone Akinniyi, jigon PDP ya yi hasashen cewa Asue Ighodalo zai samu gagarumin rinjaye a zaben gwamnan jihar Edo
  • Akinniyi ya ce Ighodalo na da goyon bayan mutanen birni da karkara da kuma manyan gari wanda hakan zai ba shi nasara a zaben
  • Da ya ke tattaunawa da Legit.ng, Akinniyi ya ce Ighodalo zai lallasa abokin hamayyarsa, Sanata Monday Okpebolo na APC cikin sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Dare Glintstone Akinniyi, mai magana da yawun kungiyar matasan jam’iyyar PDP ta kasa ya yi hasashen dan takarar da zai lashe zaben jihar Edo.

Dare Akinniyi ya yi hasashen cewa Asue Ighodalo ne zai lashe zaben gwamnan Edo da za a gudanar a yau Asabar 21 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya tsawatarwa 'yan siyasa ana saura awanni a yi zaben Edo

Jigon PDP ya yi hasashen makomar zaben gwamnan jihar Edo na yau Asabar
Jigon PDP ya yi hasashen wanda zai lashe zaben gwamnan Edo. Hoto: Senator Monday Okpebholo, Asue Ighodalo
Asali: Facebook

Akinniyi: "Ighodalo zai lallasa Okpebolo"

A wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da shi a ranar Juma’a, Akinniyi ya bayyana cewa Ighodalo zai doke abokin hamayyarsa, Sanata Monday Okpebolo na APC, domin yin nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Akinniyi, dan takarar PDP zai samu akalla kashi 75 cikin 100 na kuri’un da za a kada a ranar Asabar domin ya zama gwamnan jihar Edo.

Da yake karin haske, Akinniyi ya yi nuni da cewa hasashen nasa ba kawai canki canka ba ne, sai dai hasashe ne bisa la’akari da halin da ake ciki a jihar Edo.

'Dalilan da za su ba Ighodalo nasara'

Akinniyi ya shaidawa Legit.ng cewa:

"Asue Ighodalo na jam'iyyar PDP zai doke abokin hamayyarsa da akalla kashi 75 na yawan kuri'un da za a kada. Wannan hasashen ba canki canka ba ne.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamna 2024: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da siyasar Edo

"Za ku iya tunawa Asue Ighodalo ya zagaya kasashen duniya, inda yake zantawa da 'yan Edo game da shirye-shiryensa na jihar; kuma ya samu amincewar manyan masu ruwa da tsaki.
"Dan takarar PDP zai samu narasa cikin ruwan sanyi ba tare da la'akari da shirin APC na haifar da hargitsi ba. “Adalci, daidaito da gaskiya ne zai sa al’ummar Edo su kada kuri’a ga PDP. "

"Wanda zai lashe zaben Edo" - Malami

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa Prophet Joel Atuma na cocin The Lord Grace Provinces, Umuahia, jihar Abia, ya hango wanda zai lashe zaben jihar Edo.

Malamin addinin ya bayyana cewa akwai harafin 'E' a sunan dan takarar kuma kotu ba za ta iya sauya sakamakon zaben da hukumar INEC za ta sanar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.