Ayyukan Ban Mamaki 3 da Ahmad Aliyu Ya Kinkimo da Ya Zama Gwamnan Sokoto

Ayyukan Ban Mamaki 3 da Ahmad Aliyu Ya Kinkimo da Ya Zama Gwamnan Sokoto

Sokoto - A karshen Mayun 2023 ne Alhaji Ahmad Aliyu ya karbi mulki a matsayin gwamna mai cikakken iko a jihar Sokoto.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Gwamna Ahmad Aliyu ya gaji tsohon mai gidansa, Aminu Waziri Tambuwal wanda ya karasa mulkinsa a jam’iyyar PDP.

Abubuwa da-dama sun faru bayan APC ta karbi ragamar shugabanci daga hannun APC a Sokoto daga 2023 zuwa yanzu.

Gwamnan Sokoto
Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu ya na jawo abin suka a mulki Hoto: @AhmadAliyuSkt, @Topboychriss, fouranchors.org
Asali: Twitter

Ayyukan gwamnan Sokoto da suka jawo magana

A rahoton nan, Legit Hausa ta kawo wasu ayyukan gwamna Ahmad Aliyu da suka jawo surutu a ciki har da wajen Sokoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Motocin hayan N3.4bn a Sokoto

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Tinubu ya iske a ofis da suka hana shi zuwa taron Majalisar dinkin duniya

An kashe makudan kudi domin samar da motocin Toyota Camry XSE na zamani da za a rika haya da su a jihar da ke kukan talauci.

Rahoton VON ya ce N3.4bn aka kashe domin sayo motocin Toyota Camry da manyan bas domin daukar mata a cikin birnin Sokoto.

Masu sukar Ahmad Aliyu sun ce gwamnatinsa ba ta san abin da yake yi mata ciwo ba.

2. Aikin rijiyoyin zamanin N1.2bn

Gwamnatin Sokoto ta yi ikirarin kashe Naira biliyan 1.2 domin a gyara rijiyoyin burtsatsi na zamani da nufin a samar da ruwa.

Daga baya Punch ta ce an yi karin haske inda gwamna Ahmad Aliyu ya ce ginin hadin-guiwa ne da bankin duniya da wasunsu.

Duk da an fahimci ginin rijiyoyi aka yi ba gyara ba, wasu sun soki adadin kudin.

3. Shingen kan titunan Sokoto a N800m

The Guardian ta ce PDP ta zargi gwamna Ahmad Aliyu da ware N30bn domin aikin gina shinge a kan wasu titunan da ke Sokoto.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da za su iya jawo jam'iyyar PDP ta faɗi a zaɓen gwamnan jihar Edo

Gwamnatin APC ta karyata zancen tare da bayyana cewa N800m kadai za a kashe domin wannan aiki da zai kare rayukan jama’a.

A labarin nan, gwamnatin Sokoto ta zargi jam’iyyar hamayya da yada zancen karya, ta ce ana neman kauda tunanin al'umma ne.

Gwamna Abba ya sakawa masoyansa

A gefe guda, ana da labari mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf yana cigaba da rabon kayan alheri ga masoyansa a jihar Kano.

Wata yarinya da ta fasa asusu a 2019 ta ba Abba Gida Gida gudumuwar kamfe lokacin yana takara a inuwar PDP ta maida dubunsu a yau.

Masoya Alhaji Abba Kabir Yusuf su na ta samun kyaututtuka yayin da wasu ke ficewa daga Kwankwasiyya zuwa APC mai-ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng