“Na San Komai”: Tinubu Ya Magantu game da Halin Kunci, Ya Fadi Silar Shan Wahala

“Na San Komai”: Tinubu Ya Magantu game da Halin Kunci, Ya Fadi Silar Shan Wahala

  • Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya sani ana cikin wani hali a Najeriya inda ya zargi gwamnatocin baya
  • Tinubu ya ce dukan wannan hali da aka shiga na da nasaba da matakan da aka dauka a baya a Najeriya
  • Shugaban ya bukaci hadin kai daga masu ruwa da tsaki da sauran alumma domin ciyar da Najeriya gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya.

Tinubu ya ce duk yanayin da ake ciki yana sane sai dai ya ce laifin gwamnatocin baya ne da irin matakan da suka dauka.

Kara karanta wannan

"Kin koyi rayuwa": Gwamna ya fadi yadda aka zalunci ƴarsa a sansanin NYSC

Bola Tinubu ya yi magana kan halin kunci da yan kasa ke ciki
Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ana cikin halin kunci a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya fadi yadda Najeriya za ta gyaru

Shugaban ya fadi haka yayin ganawa da tsofaffin shugabannin Majalisar Tarayya a Abuja, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce Najeriya za ta gyaru tare da samun cigaba musamman idan aka samu hadin kai.

"Duk da bambancin jam'iyya a baya da kuma yanzu, kun cigaba da amincewa da ni da tsarin da muke da shi kan Najeriya."
"Ina muku godiya, babu wanda zai yi fiye da mu, na zagaya kasashen duniya na ga yadda suka samu cigaba ta hanyar hadin kai."
"Tabbas akwai kunci a kasa, amma ya aka yi muka samu kanmu a ciki? mene muka yi da muke da damar samar da danyen man mai"?

- Bola Tinubu

Tinubu ya ce an bar al'umma tare da mantawa da ba matasa kyakkyawar rayuwa domin inganta rayuwarsu.

Kara karanta wannan

"Ku daina neman taimakon Ubangiji": Tsohon Minista ya shawarci yan siyasa

Ya ce an manta ba a ba yara ilimi ba inda ya ce dukan makarantu sun lalace tare da cewa dole sai an inganta su, Premium Times ta ruwaito.

"Za mu yi ta korafi daga nan har tashin kiyama yara ba su zuwa makaranta, amma mun yi wani abu kan haka domin ba su karfin guiwa? dole ne mu tambayi kanmu."

- Bola Tinubu

Gwamnati ta shirya biyan albashin N70,000

Kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fadi lokacin fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 bayan ta amince da hakan a Najeriya.

Kwamitin tsarawa da gyara albashin ma'aikata (NSIWC) ya yi zama na musamman kan fara biyan mafi ƙarancin albashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.