Ambaliya: Gwamna Zulum Ya Fadi Jaruman da Suka Rage Aukuwar Asarar Rayuka

Ambaliya: Gwamna Zulum Ya Fadi Jaruman da Suka Rage Aukuwar Asarar Rayuka

  • Gwamnatin Borno ta jinjina wa dakarun sojojin kasar nan kan yadda su ka taimaka masu da ambaliyar da ta girgiza babban birnin jihar
  • Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya mika godiyar yayin da ya karbi bakuncin babban hafsan sojan kasar nan, Janar Chistopher Musa
  • A ziyarar da Janar Christopher Musa ya kai Maiduguri, gwamna Zulum ya shaida masa sojoji sun yi namijin kokarinsu wajen ceton rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno: Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno ya jinjina wa dakarun rundunar sojan kasar nan saboda namijin kokarinsu wajen ceton rayuka.

Lamarin ya biyo bayan yadda ambaliya ta rutsa da dubunnan jama'a a Maiduguri sakamakon mummunar ambaliya a yankin.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: 'Yan siyasa sun zabura, majalisar wakilai ta tallafa da N100m

Borno
Gwamnatin Borno ta gode wa jarumtar sojoji lokacin ambaliya Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa dakarun rundunar sojan sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen tsamo jama'a daga cikin babban hadari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Borno , Zulum ya jinjina wa sojoji

A ganawar da Farfesa Zulum ya yi da babban hafsan sojan kasar nan, Janar Christopher Musa, ya jinjina da sadaukarwa irinta sojojin kasar nan.

Ya kara da cewa taimakonsu ya agaza wajen ceto rayuka, da rage adadin wadanda rayuwarsu ka iya salwanta a ambaliyar da aka wayi Talata da ita.

Gwamna Zulum ya gode wa sojoji

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya gode wa dakarun sojojin kasar nan bisa taimakon da su ke bayar wa a jihar Borno ta fuskoki da dama.

Zulum ya kara da cewa yanzu haka an samu raguwar rashin tsaro a Borno da akalla 90% saboda jajircewar dakarun wajen tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Yan majalisar dattawa sun ziyarci Borno, sun mika tallafin N74m

Kwankwaso ya ba gwamnan Borno agajin ambaliya

A baya kun ji cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai ziyarar jaje zuwa Maiduguri, babban birnin Borno sakamakon ambaliya.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayar da agajin Naira Miliyan 50 a matsayin gudunmawa domin a kara taimakon jama'ar da ambaliya ta rutsa da su a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.