An Cafke Dan Ta’adda Mai Nuna Bindiga a Intanet da Gungun Yan Fashi a Arewa
- Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Katsina ta yi nasarar cafke gungun yan ta'addan da suka addabi al'umma a Arewa
- An ruwaito cewa yan ta'addar suna fashi da makami a kan hanya inda suke tare mutane suna kwace musu kudi da kayayyaki
- Rundunar yan sanda ta kwace tarin kayayyakin miliyoyi da yan ta'addar suka kwace a hannun mutane a wurare daban daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Rundunar yan sanda ta yi nasara a kan wani gungun yan ta'adda a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.
Rundunar yan sanda ta zargi yan ta'addar da aikata laifuffuka da dama ciki har da fashi da makami da toshe hanya.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa yan sanda sun kama yan ta'addar ne bayan sun samu bayanan sirri a kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama mai nuna bindiga a intanet
Punch ta ruwaito cewa rundunar yan sanda ta kama wani matashi a Katsina da ya dauki hotunansa da bindiga ya tura a kafafen sadarwa yana alfahari a watan Agusta.
Matashin mai suna Junaidu Yusuf ya bayyanawa yan sanda wajen da ya sayi bindigar wanda a sanadiyyar haka aka kama mutane biyu.
An kama gungun yan fashi a Arewa
Kakakin rundunar yan sanda a jihar Katsina, Sadiq Abubakar ya sanar da cewa sun kama wasu manyan yan ta'adda guda bakwai.
Sadiq Abubakar ya ce ana zargin yan ta'addar da ayyukan fashi da makami a jihohin Arewacin Najeriya.
Ayyukan da yan fashin ke yi a Arewa
Kakakin yan sanda ya tabbatar da cewa an kama yan ta'addar ne suna fashi da makami a kan hanyar Kano zuwa Zariya.
Ana zargin yan ta'addar da amfani da motoci wajen sace sace a wurare da dama ciki har da satar kayan abinci.
Kayan da aka kama wajen yan fashin
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa an kama yan ta'addar dauke da zannuwa turmi 96 wadanda kudinsu ya kai N4m.
Haka zalika yan sanda sun bayyana cewa an same su da hatsi da man gyada a cikin motocin da suke amfani da su wajen yin ta'addanci.
An kama masu taimakon yan ta'adda
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kara samun nasara a kan masu taimaka wa 'yan ta'adda da bayanan sirri domin kai hare-hare.
Daga cikin wadanda aka kama akwai yaro mai shekar 13, Umar Hassan da wani mai shekaru 70 Lawai Umaru da karin mutum biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng