'Yan Bindiga Sun Bankawa Motoci Wuta a Gidan Man Gwamna a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Bankawa Motoci Wuta a Gidan Man Gwamna a Najeriya

  • Ƴan bindiga sun kai hari gidan man Pinnacle mallakin Gwamna Peter Mbah a jihar Enugu, sun ƙona motoci huɗu
  • Rahotanni sun nuna ƴan bindigar sun karɓi fanfon mai daga hannun ma'aikacin gidan man, suka fesa wa motocin da suka ƙona
  • Lamarin dai ya haifar da firgici a tsakanin mazuana yankin yau Jumu'a, ƴan sanda sun toshe titin da lamarin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan kungiyar aware ne (IPOB) sun bankawa gidan man Pinnacle wuta a jihar Enugu.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na safiyar yau Jumu'a, 20 ga watan Satumba, 2024 a titin Agbani da ke cikin birnin Enugu.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamna 2024: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da siyasar Edo

Gwamna Peter Mbah na Enugu.
Yan bindiga sun bankawa gidan mai wuta, sun ƙone motoci a Enugu Hoto: Peter Mbah
Asali: Facebook

Kamar yadda rahoton The Nation ya kawo, maharan sun ƙona akalla motoci huɗu na abokan hulda da suka shiga gidan domin sayen fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a gidan mai

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigar waɗanda ba su wuce su huɗu ba sun kutsa cikin gidan man a wata mota ƙirar Toyota Corolla.

An ce maharan sun kwace fanfon mai, suka yi wa motocin da ke kusa wanka da fetur, sannan suka cinna masu wuta.

Haka nan kuma maharan sun zuba fetur a wata jarka mai cin lita 25, sannan suka zubawa wasu motoci da aka wanke a gidan man, suka banka masu wuta.

Wane mataki mahukunta suka ɗauka

Tuni jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Enugu su ka dira wurin, inda suka fara kokarin kashe wutar kafin ta yaɗu.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya 'kashe' budurwar da zai aura Naja'atu Ahmad a jihar Kano

Rahotanni sun nuna cewa motoci huɗu daga cikin waɗanɗa maharan suka cinna wa wuta sun ƙone ƙurmus.

Lamarin dai ya haifar da firgici a yankin, wanda ya tilasta wa masu kasuwanci a kewayen gidan man rufe wuraren sana'o'insu, tare da komawa gida.

Ƴan sanda sun rufe titin Agbani, bisa tilas direbobin mota suka canza hanya domin zuwa tashar Nise

Wannan shi ne karo na biyu da ‘yan bindiga suka kai hari gidan man Pinnacle, mallakin Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu.

Ƴan bindiga sun kashe ɗan kasuwa a Enugu

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Enugu a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Enugu ta Kudu.

Labari ya zo cewa miyagun ƴan bindigan sun hallaka shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Ogbete bayan sun binidige shi har lahira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262