Gangamin Zanga Zanga: Kungiyoyi 60 Sun Barranta da Fitowa Titi a Ranar 1 ga Oktoba

Gangamin Zanga Zanga: Kungiyoyi 60 Sun Barranta da Fitowa Titi a Ranar 1 ga Oktoba

  • Kungiyoyin matasa akalla 60 ne su ka ga rashin dacewar gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Bola Tinubu
  • A ranar 1 ga Oktoba da ake bikin zagoyowar yancin kai ne wasu matasa su ka shirya fita nuna fushinsu da manufofin gwamnati
  • Kungiyoyin da su ka hada da na Arewaci da Kudancin kasar nan amma sun ce ba da su ba, yayin da su ka shawarci matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Jagororin kungiyoyin matasa sama da 60 sun janye daga shiga gagarumin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin tarayya.

Wasu matasa a kasar nan na shirin yadda za a kwararo titunan kasar nan ranar 1 Oktoba, 2024 domin bayyana rashin gamsuwa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da kasar nan.

Kara karanta wannan

Kuɗin fetur: Yan kwadago sun raina sabon albashin N70,000, za su sake bugawa da Tinubu

Tinubu
Matasa sama da 60 sun janye daga zanga zangar 1 Oktoba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian a wallafa cewa jagoran kungiyar Nigeria Youth Organisation, Duke Alamboye shi ne ya bayyana janyewar a ziyarar da suka kai ofishin mai kula da shirin afuwa na gwamnatin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin da su ka janye shiga zanga zanga

Shugaban ofishin kula da shirin afuwa na gwamnatin tarayya, Dr. Dennis Otuaro, ya bayyana cewa kungiyoyin kasar nan sun mara wa gwamnatin kasar nan baya.

The Vanguard ta wallafa cewa daga cikin kungiyoyin da su ka janye akwai National Youth Congress, Arewa Youth Council, Yoruba Youth Council, Ohaneze Youth Council da South-South Advocate da sauransu.

Zanga zanga: Kungiyoyi za su tattauna da matasa

Mista Duke Alamboye ya ba wa gwamnatin tarayya tabbacin za su yi aiki tare da sauran kungiyoyi wajen jan hankalin matasa yar da maganar zanga zanga.

Kara karanta wannan

Bayan tallafin biliyoyi, gwamnatin Borno ta fitar da gudunmawar ambaliya da ta samu

Ya ce daga cikin dabarun da za su dauka domin cimma hakan akwai wayar da kan matasan ta kafafen yada labarai.

Masu zanga zanga sun yi nasara a kotu

A baya mun ruwaito cewa matasan kasar nan da ke shirin gudanar da zanga-zangar adawa ga manufofin gwamnatin tarayya, inda kotu ta ba su damar ci gaba da bayyana fushinsu a kasar nan.

Tun da farko, wasu mutum 16 ne su ka shigar da kara kotu su ne neman kotu ta haramta wa matasan gudanar da zanga-zanga domin shaida wa shugaba Tinubu mawuyacin halin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.