Gwamnan Zamfara Ya Tura Tallafin Miliyoyi ga Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Maiduguri

Gwamnan Zamfara Ya Tura Tallafin Miliyoyi ga Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Maiduguri

  • Gwamnan jihar Zamfara ya tura tawaga ta musaamman zuwa Maiduguri domin jajantawa waɗanda albaliyar ruwa ta shafa
  • Dauda Lawal ya kuma tura da saƙon tallafin N100m ga waɗanda ibtila'in ya shafa tare da addu'ar Allah ya ji ƙan waɗanda suka rasu
  • Tawagar da gwamnan ya tura ta ƙunshi manyan ƙusoshin gwamnatin Zamfara ƙarƙashin jagorancin sakatare, Abubakar Nakwada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jajantawa gwamnati da al’ummar Borno bisa mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri.

Gwamna Lawal ya miƙa sakon jaje ne ta hannun tawagar wakilan da ya aika Maiduguri ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin Zamfara, Mallam Abubakar Nakwada.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi tsohon gwamnan da yake zargi da alaƙa da ƴan bindiga

Gwamna Dauda Lawal.
Maiduguri: Gwamnan Zamfara ya ba wadanda ambaliya ta shafa tallafin N100m Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Gwamna Lawal ya tura tawaga Maiduguri

Channels tv ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Idris ya fitar ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa makasudin ziyarar shi ne jajantawa gwamnatin Borno kan ambaliyar ruwan da ta faru mai taɓa zuciya.

Yayin da yake isar da sakon Gwamna Lawal a fadar gwamnatin Borno, Malam Abubakar Nakwada ya miƙa tallafin da gwamnatin jihar Zamfara ta bayar na N100m.

Gwamnan Zamfara ya miƙa tallafin N100m

"A madadin al’umma da gwamnatin Zamfara, muna muna miƙa sakon jaje game da mummunar ambaliyar da ta afku sakamakon kwararar ruwa daga madatsar ruwa ta Alu da ke Maiduguri.
"Mun yi matukar kaɗuwa da jimami bayan samun rahotan sama da mutane miliyan daya ne suka rasa muhallansu sakamakon wannan bala'i. Muna addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahun takwarorinsa a shirin fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000

"Domin nuna goyon baya gwamnatin Zamfara ta bada gudunmawar N100m don tallafawa waɗanda lamarin ya shafa a Maiduguri."

- Mallam Abubakar Nakwada.

Ya ƙara da addu'ar Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ci gaba da kawo taimako ga wadanda abin ya shafa kuma Ya ba su karfin gwiwa da juriya wajen sake gina rayuwarsu, in ji Punch.

Kwankwaso ya kai ziyara Maiduguri

A wani rahoton kuma, dan takarar shugaban kasa a 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso ya ziyarci Maiduguri domin taya gwamna Babagana Zulum alhini.

Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan Kano ne ya bayyana bakin cikinsa kan afakuwar ambaliya da ta shafi sama da mutum miliyan biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262