Gina Shingen N30bn: Gwamnatin Sakkwato Ta Zargi PDP da Yada Karya kan Kwangila

Gina Shingen N30bn: Gwamnatin Sakkwato Ta Zargi PDP da Yada Karya kan Kwangila

  • Gwamnatin jihar Sakkwato ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yada karya kan ayyukan da ta ke yi wa jamaa
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya zargi PDP da daukar nauyin yada labaran karya kan kwangilar shingen titunan jihar
  • Martanin na zuwa bayan PDP ta nemi hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta bincike gwamnatin Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Gwamnatin Ahmed Aliyu ta jihar Sakkwato ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yada karya da daukar nauyin rahotannin kage.

Gwamnatin na ce PDP na fafutukar kawar da hankalin gwamnatin Ahmed Aliyu daga gudanar da ayyukan ci gaba da raya kasa da inganta rayuwar yan Sakkwato.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Majalisar amintattun PDP ta shiga ganawar gaggawa

Sakkwato
Gwamnatin Sakkwato ta yi martani kan zargin kwangilar shingen hanya kan N30bn Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa babban sakataren yada labaran gwamnan Sakkwato, Abubakar Bawa, ya ce sun gano dabarun PDP na hana gwamnatinsu aiki a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"PDP na mana kage:" Gwamnatin Sakkwato

Sanarwar da Abubakar Bawa ya fitar ta ce babu maganar bayar da kwangilar N30bn da ake zargin gwamnatin Sakkwato ta yi domin gina shinge a titunan jihar.

Gwamnatin ta ce abin da ke akwai shi ne kwangilar N800m na sanya shinge a manyan titunan jihar wanda ake bukata saboda kare rayukan dalibai.

Gwamnatin Sakkwato ta zargi PDP da hassada

Gwamnatin Ahmed Aliyu ta jihar Sakkwato ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yi mata bakin cikin ayyukan ci gaban da ake samu a jihar.

Ta zargi PDP da jawo koma baya bayan shafe shekaru takwas ta na mulkin Sakkwato, inda ta ce hassada kawai ta ke yi wa jama'a.

Kara karanta wannan

PDP ta gaji da lamarin gwamnan Sokoto, ta bukaci EFCC ta binciki N30bn da ya ware

Sakkwato: PDP ta yi maganar binciken Tambuwal

A baya mun ruwaito cewa jam'iyyar hamayya ta PDP ta caccaki gwamnatin Sakkwato bisa bullo da zancen zargin da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal.

Gwamnatin jihar na zargin tsohon gwamna Tambuwal da karkatar da kudin hannun jari da ya kai N16.1bn, lamarin da PDP ta ce a shirye su ke su kare kansu bisa zargin da ake yi masu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.