Zaben Edo: Yiaga Africa Ta Lissafa Garuruwa 8 da Ka Iya Fuskantar Tashin Hankula

Zaben Edo: Yiaga Africa Ta Lissafa Garuruwa 8 da Ka Iya Fuskantar Tashin Hankula

  • Kungiyar Yiaga Africa ta yi hasashen cewa za a iya samun tashe-tashen hankula a wasu kananan hukumomi takwas na jihar Edo
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin da ta ke tsokaci kan zaben gwamnan Edo na 2024 da za a gudanar ranar Asabar, 21 ga Satumba
  • Yiaga Africa ta kuma nuna damuwarta kan cewa za a iya amfani da tashin hankali wajen murkushe masu zabe ko sauya sakamako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Yiaga Africa ta lissafa kananan hukumomi takwas daga cikin kananan hukumomi 18 na Edo a matsayin wuraren da ke iya fuskantar tashe-tashen hankula.

Kungiyar ta yi kira ga mahukunta da su dauki kwararan matakan tabbatar da an gudanar da zaben gwamnan Edo na ranar Asabar cikin lumana.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamna 2024: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da siyasar Edo

Yiaga Africa ta yi magana kan zaben gwamnan jihar Edo na ranar Asabar
Zaben Edo: Yiaga Africa ta hango tashin hankul a kananan hukumomi 8.
Asali: Original

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Yiaga Africa ta fitar a ranar Alhamis kan shirye-shiryen zaben jihar na Edo, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yiaga Africa ta magantu kan zaben Edo

An ce Dakta Aisha Abdullahi, shugabar sa ido kan harkokin zaben Edo da kuma Samson Itodo, babban daraktan Yiaga Africa ne suka fitar da sanarwar tare.

Ana zargin zaben zai iya fuskantar tashe-tashen hankula musamman bayan kin amincewa jam'iyyar PDP da dan takararta na sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Yiaga Africa ta bayyana cewa zaben Edo zai kasance tamkar ma'auni ne wajen tantance kudirin kasar Najeriya na tabbatar da ingancin zabe.

Tashe tashen hankula a zaben Edo

Jaridar The Cable ta nuna damuwa cewa za a iya amfani da tashin hankali da tsoratarwa domin murkushe masu kada kuri'a a wasu garuruwa.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Jerin yan takara 17 da suke neman kujerar gwamna

Hakazalika Yiaga Africa ta bayyana damuwarta kan yiwuwar a samu wadanda za su dakile jigilar kayan zabe na INEC ko kuma kawo cikas ga bayyana sakamakon zabe.

Kungiyar ta bayyana wadannan kananan hukumomin a matsayin wuraren da ka iya fuskantar tashin hankula: Ikpoba/Okha, Oredo, Egor da kuma Ovia ta Kudu maso Yamma.

Sauran kananan hukumomin su ne: Ovia ta Arewa maso Gabas, Esan ta Kudu maso Gabas, Etsako ya Yamma da Etsako ta Gabas.

"Wanda zai lashe zaben Edo" - Malami

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani malamin addini ya hango dan takarar da zai lashe zaben gwamnan jihar Edo da za a gudanar ranar Asabar 21 ga watan Satumba.

Prophet Joel Atuma na cocin The Lord Grace Provinces, ya bayyana cewa dan takarar da ba a tsammani ne zai samu nasara kuma akwai harafin 'E' a sunasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.