Ana Tsaka da Jajantawa Maiduguri, Ambaliya Ta Sake Yin Barna a wata Jihar Arewa

Ana Tsaka da Jajantawa Maiduguri, Ambaliya Ta Sake Yin Barna a wata Jihar Arewa

  • Mazauna al’ummar Bode Sa’adu da ke Moro a jihar Kwara a halin yanzu sun fara kaura daga gidajensu biyo bayan ambaliyar ruwa
  • An ce ambaliyar ruwa ta mamaye garin Bode Sa'adu sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka daga ranar Talata zuwa Alhamis
  • Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyara garin Bode Sa'adu inda ya jajantawa al'umma da kuma duba barnar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Gidaje da dama da wasu kadarori da suka hada da amfanin gona, sun dulmiye a ruwa a garin Bode Sa'adu, hedikwatar karamar hukumar Moro ta jihar Kwara.

An rahoto cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a yankin a ranar Talata zuwa Alhamis ya jawo ambaliya wadda ta mamaye garin Bode Sa'adu.

Kara karanta wannan

Yadda mutane sama da 100 su ka rasu a manyan iftila'I 4 a Arewacin Najeriya

Gwamnatin jihar Kwara ta yi magana kan ambaliyar ruwa a garin Bode Sa'adu
Ambaliya ta mamaye garin Bode Sa'adu da ke jihar Kwara. Hoto: Justin Sullivan
Asali: Getty Images

Ambaliya ta afku a jihar Kwara

Sai dai jaridar Punch ta tattaro a ranar Alhamis cewa ba a rasa rayuka a ambaliyar da ta tilasta gwamnan jihar, Mallam AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyara yankin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce ana zargin ambaliyar ta kafku ne sakamakon aikin mayar da hanyar Ilorin-Jebba-Mokwa zuwa hannu biyu da gwamnatin tarayya ta yi.

An tattaro cewa ambaliyar ta yi kamari ne sakamakon mamakon ruwan sama a yammacin Laraba da aka kwashe sama da sa'o'i biyar ana yi.

Mazauna yankin, sun fara yin ƙaura daga gidajensu zuwa wajen 'yan uwansu da ke a wasu garuruwan da ambaliyar ba ta shafa ba yayin da suka bar kayayyakinsu a baya.

Gwamna ya ziyarci Bode Sa'adu

Jaridar Vanguard ta rahoto Gwamna AbdulRazaq ya ziyarci al’ummar Bode Sa’adu ne a ranar Alhamis domin jajanta wa mutanen yankin biyo bayan wannan ambaliya.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Dattijon attajiri, Dantata ya tallafa wa Borno da sama da Naira biliyan 1

Gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan ayyuka na musamman John Bello da kuma mai ba da shawara ta musamman (kan ayyuka na musamman), Abdulrazaq Jiddah.

“Mun zo nan ne domin jajanta wa al’ummar Bode Sa’adu tare da tabbatar da cewa kowa yana cikin koshin lafiya da kuma duba musabbabin ambaliyar.”

- A cewar gwamnan.

Borno ta samu tallafin ambaliya

A wani rahoton, mun ruwaito cewa akalla gwamnatocin jihohi 9 ne suka tarawa jihar Borno Naira biliyan 1.1 a matsayin gudunmawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

Gwamnatocin jihohin sun kaiwa jihar Borno wannan tallafi ne a lokuta daban daban, idan muka tattaro bayani na kudin da kowanne gwamna ya bayar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.