Rai Ɓakon Duniya: Hadimin Gwamna Dikko Radda Ya Kwanta Dama a Katsina

Rai Ɓakon Duniya: Hadimin Gwamna Dikko Radda Ya Kwanta Dama a Katsina

  • Hadimin gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda a bangaren harkokin matasa ya riga mu gidan gaskiya
  • An tabbatar da rasuwar marigayin mai suna Aminu Lawal Custom a yau Alhamis 19 ga watan Satumbar 2024
  • Kafin rasuwar marigayin, yana daga cikin masu neman takarar shugaban karamar hukumar Malumfashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - An shiga alhini bayan rasuwar hadimin Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina.

Marigayin mai suna Aminu Lawal Custom ya rasu ne a yau Alhamis 19 ga watan Satumbar 2024 a karamar hukumar Malumfashi.

Hadimin Gwamna Dikko Radda ya rasu a Katsina
Hadimin Gwamna Dikko Radda mai suna Aminu Lawal ya kwanta dama a Katsina. Hoto: Umaru Dikko Radda.
Asali: Twitter

Mukamin da marigayin ya rike kafin rasuwarsa

Punch ta ruwaito cewa kafin rasuwar marigayin, shi ne hadimin Gwamna Umaru Radda a bangaren harkokin matasa.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamna Radda ya yi ruwan miliyoyi ga talakawan Maiduguri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin har ila yau, yana daya daga cikin masu neman takarar shugabancin karamar hukuma a karkashin APC.

Gwamna Radda ya jajantawa iyalan marigayin

Gwamna Umaru Radda ya yi alhinin rasuwar matashin inda ya ce mutum ne mai kwazo wurin taimakon al'umma.

Sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahim Mohammed shi ya tabbatar da haka ga yan jaridu a yau Alhamis 19 ga watan Satumbar 2024.

Ibrahim ya ce gwamnan ya kadu matuƙa da rashin matashin mai kwazo da kuma hangen nesa inda ya ce gaba daya jihar sun rasa mai son cigaban matasa.

Radda ya ce wannan rashi ba ga iya iyalan marigayin kadai ba ne hatta al'ummar Malumfashi da jihar sun yi babban rashi.

Radda ya fadi gudunmawar marigayin a Katsina

"Aminu Lawal Custom mutum ne jajirtacce kuma mai son cigaban matasa a jihar baki daya."

Kara karanta wannan

Watanni 3 kacal da nada su, gwamna ya fatattaki shugaban karamar hukuma

"Irin gudunmawar da ya ba gwamnatinmu da karamar hukumar Malumfashi ba za mu taba mantawa ba."

- Cewar sanarwar

Gwamnan Katsina ya warewa ruwa N22bn

Kun ji cewa Gwamnatin Katsina ta ware kuɗi N22bn domin aikin samar da wadataccen ruwan sha a faɗin kananan hukumomi 34.

Shugaban hukumar ruwa ta Katsina, Tukur Hassan ya bayyana haka inda ya ce aikin zai kawo ƙarshen ƙarancin ruwa da rashin tsaftarsa.

Wannan aiki za a yi shi ne karkashin kulawar wani shiri na haɗin guiwa tsakanin gwamnatin Katsina da bankin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.