NECO Ta Fitar da Sakamakon Jarrabawar 2024, An Yi Bayanin Ka'idojin Dubawa
- Hukumar kula da jarabawa a Najeriya (NECO) ta tabbatar da sake sakamakon jarrabawar dalibai da aka yi kwanakin baya
- Magatakardar hukumar NECO, Farfesa Dantani Wushishi shi ya tabbatar da haka ga yan jaridu a birnin Minna na jihar Niger
- Wushishi ya ce an samu matsaloli da dama kama daga satar jarabawa a makarantu da kuma cin hanci da rashawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar kula da jarabawa ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarrabawar dalibai.
Hukumar da ke da hedkwata a Minna na jihar Niger ta fitar da sakamakon ne a yau Alhamis 18 ga watan Satumbar 2024.
NECO ta saki sakamakon jarrabawar dalibai
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardar hukumar, Farfesa Dantani Wushishi ya tabbatar, cewar rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wushishi ya bayyana cewa hukumar ta dakatar da wata makaranta a jihar Ekiti saboda satar amsa.
Har ila yau, ya ce sun dauki mataki kan masu kula da jarabawar mutum 21 a jihohi 12 da ke Najeriya, cewar jaridar Thisday.
Yadda za a duba sakamakon jarrabawar NECO
Matakin farko da dalibai za su dauka shi ne ziyartar shafin hukumar na yanar gizo. Ana so dalibai su ziyarci shafin NECO: www.neco.gov.ng.
Na biyu, dalibai za su sayi wata lambar sirri ta musamman a shafin NECO da za su yi amfani da ita wajen duba sakamakon NECO ta 2024.
Sannan dalibai za su ziyarci sashen duba sakamakon jarabawar a shafin yanar gizo inda za su shiga shafin ta hanyar amfani da shekarar da suka zana jarabawa.
Matakin na hudu shi ne shigar da shekarar jarabawa (2024) da kuma nau'in jarabawar (June/July SSCE) da kuma shigar da lambobi 10 na jarwarsu ta NECO.
Sai mataki na karshe, dalibai za su danna maɓallin "Duba Sakamakon" domin duba sakamakon jarabawarsu ta NECO. Za a nuna sakamakon nan take.
An jero matakan duba jarabawar NECO
Kun ji cewa duka wadanda suka zana jarabawar NECO ta 2024 za su iya duba sakamakonsu ta hanyar ziyartar shafin hukumar na yanar gizo.
Daliban da suka zana NECO kuma suke son duba sakamakonsu, za su yi amfani da lambar rajista, lambar sirri da shekarar jarrabawar.
A rahoton nan, Legit Hausa ta samar da matakai daki-daki na yadda dalibai za su iya duba sakamakon jarabawarsu cikin sauki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng