Rashin Tsaro: Rundunar Yan Sanda Ta Sake Shiri Domin Dakile Yan Ta’adda
- Sufeton yan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun ya yi garanbawul ga manyan jami'an tsaro a wasu jihohin Najeriya
- IGP Kayode Egbetokun ya ba da umarnin canza kwamishinonin yan sanda a jihohin Rivers, Delta da kuma birnin tarayya Abuja
- Kayode Egbetokun ya yi umarni ga jami'an tsaron wajen dagewa da aiki kan yakar yan ta'adda masu cutar da mutane a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sufeton yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya yi canje canje a rundunar yan sanda.
IGP Kayode Egbetokun ya yi kira ga jami'an tsaron kan dagewa wajen yakar miyagu a dukkan sassan Najeriya.
Rundunar yan sanda ne ta bayyana haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A canza kwamishinonin yan sanda a Najeriya
IGP Kayode Egbetokun ya mayar da kwamishinan yan sandan Rivers, Olatunji Disu zuwa birnin tarayya Abuja.
Haka zalika, IGP Kayode ya canza CP Abaniwonda Olufemi daga jihar Delta zuwa matsayin kwamishinan yan sanda a jihar Rivers.
A daya bangaren, sufeton yan sandan ya amince da canza CP Peter Opara daga birnin tarayya Abuja zuwa jihar Delta.
IGP ya nada kwamishinonin yan sanda
IGP Kayode Egbetokun ya amince da naga kwamishinonin yan sanda a jihohin Abia, Legas, Ebonyi da kuma Akwa Ibom.
Jaridar the Nation ta wallafa cewa IGP Kayode Egbetokun ya yi kira ga manyan yan sandan da su yi kokari wajen yaki da ta'addanci domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.
Haka zalika, IGP Kayode Egbetokun ya bukaci su zama jakadu da za su inganta aikin dan sanda domin kawo cigaba a Najeriya baki daya.
CP Garba Salman zai dakile yan ta'adda
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta dauko hanyar magance karuwar ayyukan bata gari da fadan dabanci da yake neman ya dawo a halin yanzu.
Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Garba Salman ya ba jami'ansa umarnin su rika sinitiri a kullu yaumin kuma a kowane lokaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng