Rikicin Cikin Gida: Majalisar Amintattun PDP Ta Shiga Ganawar Gaggawa

Rikicin Cikin Gida: Majalisar Amintattun PDP Ta Shiga Ganawar Gaggawa

  • Majalisar amintattu na PDP (BoT), ta shiga ganawar gaggawa domin gano matsalolin da su ke addabi jam'iyyar
  • Tun zaben 2023 ne PDP ke fuskanatar matsaloli da dama, musamman da jigo a jam'iyyar, Nyesom Wike yake yin fuska biyu
  • Gabanin taron na yau, gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa za a warware matsalar da PDP ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Majalisar amintattu ta jam'iyyar PDP ta shiga ganawar sirri cikin gaggawa da jiga-jiganta da ke majalisar kasar nan.

Tun bayan kammala babban zaben 2023 ne PDP ke fuskantar matsalolin cikin gida wanda ta ke ganin zai zama barazana gare ta a gaba.

Kara karanta wannan

"In Sha Allahu za mu ɗinke ɓaraka," Gwamna ya gano waɗanda suka haddasa rikici a PDP

Jam'iyya
PDP ta shiga taron gaggawa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa wasu na ganin shugaban riko na PDP, Umar Damagum ya gaza hada kan 'ya'yan jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin jam'iyyar PDP ke kamari

Pulse Nigeria ta wallafa cewa rikicin da ke kara kamari tsakanin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya rikita PDP da jawo baraka.

Lamari ya kara tabarbare wa tun lokacin da Minista Wike ya kara jan kunnen gwamnonin PDP kan su daina tsoma baki kan rikicin Ribas.

Nyesom Wike ya zamar wa PDP karfen kafa bayan ya karbi mukami a gwamnatin APC, sannan ya ki fita daga jam'iyyarsa.

PDP na kokarin magance rikicinta

Shugaban kwamitin amintattu na PDP, Adolphus Nwabara da sakatarensa, Sanata Ahmed Makarfi sun yi tattaunawar sirri a ranar Talata a Abuja.

Sauran sun hada da mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Lere Oyewumi da mai tsawatarwa marasa rinjaye a majalisar wakilai, Hon. Ali Isa JC da Hon. Pastor Ojema Ojotu

Kara karanta wannan

PDP ta gaji da lamarin gwamnan Sokoto, ta bukaci EFCC ta binciki N30bn da ya ware

PDP na shirin dinke barakar gida

A baya mun ruwaito cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayyana cewa ana sa ran shawo kan matsalar da ake PDP ke fuskanta kuma za a dinke barakar.

Gwamna Bala Mohammed ya jingina matsalar da su ke fama da ita da yadda Nyesom Wike ke cin amanar PDP ta hanyar yi masu fuska biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.