Gwamnan PDP Ya Nuna Damuwa kan Rashin Samun Tallafin Shinkafar Tinubu

Gwamnan PDP Ya Nuna Damuwa kan Rashin Samun Tallafin Shinkafar Tinubu

  • Gwamnatin jihar Taraba ta fitar da sanarwa kan tallafin shinkafa da gwamnatin tarayya ta ce za ta ba dukkan jihohin Najeriya
  • Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Taraba, Savior Noku ya ce har yanzu ba su ga alamar shinkafar da aka yi musu alkawari ba
  • A ranar 15 ga watan Yuli ne ministan sadarwa ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta ba dukkan jihohin Najeriya tirelar shinkafa 20

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Gwamnatin jihar Taraba ta fitar da korafi kan shinkafa tirela 20 da gwamnatin tarayya ta yi alkawari ga jihohi.

Gwamnatin Taraba ta ce har yanzu ba ta ga alamar shinkafar ba balle kuma ta raba ga al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Karin albashi: Gwamna zai fara biyan N70,000 a watan Satumba

Gwamnan Taraba
Gwamnatin Taraba ta koka kan shinkafar Tinubu. Hot: Taraba State Government
Asali: Facebook

Leadership ta wallafa cewa tun a watan Afrilu da aka tura shinkafa jihar Taraba ba a kara tura abincin tallafi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar raba shinkafa a jihohi

A watan Yuli ne gwamnatin tarayya ta yi alkawarin raba shinkafa tirela 20 ga kowace jiha da birnin tarayya Abuja.

Ministan sadarwa da wayar da kan al'umma ya ce za a raba shinkafar ne domin rage radadin tsadar rayuwa a Najeriya.

Taraba ta ce ba ta samu shinkafa ba

Vanguard ta wallafa cewa gwamnatin jihar Taraba ta fitar da sanarwa kan cewa har yanzu ba ta samu shinkafar da aka musu alkawari ba.

Jihar Taraba ta yi korafi kan shinkafar ne bayan jihohi da dama a Najeriya sun sanar da cewa sun samu kasonsu.

Yaushe rabon Taraba da samun shinkafa?

Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Taraba, Savior Noku ya ce tun a ranar 15 ga watan Afrilu da suka samu shinkafa ba su sake samun tallafin abinci ba.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Majalisar dinkin duniya ta ba da tallafin dalolin kudi ga mutanen Maiduguri

A halin yanzu dai al'ummar jihar Taraba sun zuba ido domin ganin gwamnatin tarayya ta tura musu shinkafar kamar sauran jihohi.

Barau: 'Ana karkatar da shinkafar Tinubu'

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar kasar nan ta bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na kokarin raba tallafi domin rage radadin matsin rayuwa.

Mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ne ya bayyana haka, amma ya ce wasu daidaikun jama'a ne ke dakile kokarin shugaban kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng