Gwamnatin Tinubu Na Shirin Kare Hakkin Yan Najeriya, Za Ta Yaki Masu Tauye Mudu

Gwamnatin Tinubu Na Shirin Kare Hakkin Yan Najeriya, Za Ta Yaki Masu Tauye Mudu

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta ce ba za ta amince yan kasuwa da masu sayar da man fetur su na cutar yan kasar nan ba
  • Wannan ya sa aka samar da sashe a ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da zuba jari ta kasa da zai rika bibiyar yan kasuwa
  • Daga cikin ayyukan da sashen zai yi akwai kai samame domin tabbata ba a tauye ma'auni yayin sayar da kaya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara sa ido kan wasu 'yan kasuwa a kasar nan domin tabbatar da cewa ba a cutar masu sayen kayayyaki.

Kara karanta wannan

Matasa sun shuna wa yan sanda manyan karnuka, magana ta shiga kotu

Ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da zuba jari ta kasa ce za ta kinkimo aikin domin hana tauye mudu a lokacin da yan kasa ke fama da hauhawar farashi.

Tinubu
Gwamnati za ta hana tauye ma'auni a kasar nan Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin Bola Tinubu ba za ta lamunci wasu 'yan kasuwa su rika cutar jama'ar da ke sayen kayayyaki a kasuwanni ko gidajen mai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ya gwamnati za ta hana algus?

Ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da zuba jari ta kasa ta kafa wani sabon sashen gwaji da auna kayayyakin da ake sayarwa a fadin kasar nan.

A ziyarar da ya kai kamfanin mai na kasa da ke Ijora da kamfanin Olam Agri da ke Igamu a jihar Legas, daraktan sabon sashen, Adesuyi Olajide ya ce Tinubu ya damu da yan kasar nan.

Dalilin gwamnati na yaki da algus

Gwamnati ta ce ta dole ne 'yan kasuwa su rika cika ma'auni domin yi wa masu sayen kayayyaki adalci.

Kara karanta wannan

Kotu ta dage yanke hukunci a shari'ar korar shugaban APC, Ganduje daga mukaminsa

Daraktan sashen gwaji da auna kayayyaki na ma'ikatar masana'antu, kasuwanci da zuba jari na kasa, Adesuyi Olajide ya ce za su rika ziyartar wurare bakatatan.

An shawarci gwamnati kan matsalolin Najeriya

A wani labarin kun ji yadda tsohon shugaban kasar nan, Janar AbdulSalami Abubakar ya nusar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu matsananciyar wahala da yan kasa ke fuskanta.

Janar AbdulSalami Abubakar ya ce yunwa, karuwar talauci, hauhawar farashi da sauran matsalolin da yan kasa ke ciki na kara ta'azzara, inda ya ce dole ne sai an dauki mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.