UNIMAID: Bayan Masifar Ambaliya, Jami'ar Maiduguri ta Nada Sabon Shugabanta

UNIMAID: Bayan Masifar Ambaliya, Jami'ar Maiduguri ta Nada Sabon Shugabanta

  • Hukumomi a Jami'ar Maiduguri sun nada Farfesa Mohammed Laminu Mele a matsayin sabon shugabanta
  • Farfesa Laminu Mele kafin wannan mukami shi ne ya rike mukaddashin shugaban Jami'ar na tsawon lokaci
  • Mele daga karamar hukumar Mafa a jihar Borno ya shafe fiye da shekaru 20 yana koyarwa da kuma bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno ta nada sabon shugabanta.

An nada Farfesa Mohammed Laminu Mele a matsayin shugaban Jami'ar da ke Arewa maso Gabas.

Farfesa Laminu Mele ya zama sabon shugaban Jami'ar Maiduguri
Jami'ar Maiduguri ta nada sabon shugabanta, Farfesa Laminu Mele. Hoto: Mustapha Bulama.
Asali: Facebook

An nada Farfesa Mele shugaban Jami'ar Maiduguri

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan Jami'ar, Ahmad Lawan ya fitar a jiya Laraba 18 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Borno: Manya na ci gaba da zuwa jaje Maiduguri, an ƙara bada tallafin N50m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce nadin zai fara aiki nan take inda ta ce an bi dukkan ka'idoji kafin nada Farfesan, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ahmad Lawan ya ce Farfesa Mele ya cancanci wannan mukami saboda kwarewarsa.

Farfesa Mele dan asalin karamar hukumar Mafa ne a jihar Borno wanda ke da mata da kuma yara da dama.

Mele ya shefe shekaru 20 yana koyarwa da bincike da hidima ga al'umma domin cigabansu.

Maiduguri: Mukaman da Farfesa Mele ya rike

Kafin rike wannan mukami, Mele ya rike mukaddashin shugaban Jami'ar da kuma mataimakin shugabanta a bangaren gudanarwa.

Har ila yau, Farfesa Mele ya kasance kwararre a fannin yaren Turanci wanda ya shafe shekaru da dama a tsangayar koyar da harsuna.

Sanarwar ta taya Farfesa Mele murnar samun wannan matsayi mai daraja inda ta yi masa addu'ar fatan alheri da aiwatar da aikinsa cikin nasara.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Yan majalisar dattawa sun ziyarci Borno, sun mika tallafin N74m

Ambaliyar ruwa: An rufe Jami'ar Maiduguri

Kun ji cewa ambaliyar ruwan da aka samu a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta jawo an rufe jami'ar UNIMAID .

Mahukuntan jami'ar sun sanar da hakan domin kare ɗalibai da ma'aikata sakamakon ambaliyar da ta auku.

Sun kuma miƙa saƙon jaje ga ɗalibai da ma'aikatan da ambaliyar ta ritsa da su tare da addu'ar Allah ya kiyaye gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.