Gwamna Zai Gina Gidaje Kyauta ga Wadanda Suka Samu Ambaliyar Ruwa
- Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin samar da gidaje ga mutanen da ambaliyar ruwa ta rusa musu gidaje
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa za a gina gidajen ne a dukkan kananan hukumomin jihar Kano 44
- An yi magana kan yunkurin shigar da yara yan makarantar firamare yayin da sabon zangon karatu ya fara a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi bayani kan wadanda ambaliyar ruwa ta rusa musu gidaje a Kano.
Gwamna Abba Kabir ya ce gwamnatinsa za ta samar musu da gidaje da za su cigaba da zama a jihar.
Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ambaliya: Za a gina gidaje kyauta a Kano
Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta yi alkawarin gina gidaje kyauta ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a dukkan kananan hukumomi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da lamarin ne a yayin wani zaman majalisar zartarwar jihar Kano.
Za a samar da abinci saboda ambaliya
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kara tabbatar da cewa bayan maganar gina gidaje za a samar da abinci ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamnatin ta ce hakan na cikin ƙoƙarin da ta ke wajen ganin ta rage raɗaɗin talauci da damuwa ga al'ummar jihar.
Maganar inganta ilimin yara a Kano
Gwamnatin Kano ta ce za ta samar da kayan makaranta ga dukkan yan aji daya a makarantun firamare na jihar Kano.
Bayan haka, ta ce akwai shirin samar da kujeru guda 220,000 a makarantun jihar yayin da aka fara sabon zangon karatu.
Aminu Ado ya yi jaje ga mutanen Borno
A wani rahoton, kun ji cewa sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Bayero ya jajantawa mutanen jihar Borno kan ambaliyar ruwan da ta auku.
Mai martaba Aminu Ado Bayero ya nuna kaɗuwarsa kan lamarin wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa ga al'ummar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng