Gwamna Ya Bi Sahun Takwarorinsa a Shirin Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70,000
- Gwamna Ahmed Usamn Ododo ya fara shirin fara biyan ma'aikatan jihar Kogi sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
- A ranar Laraba da ta gabata, gwamnatin Ododo ta kafa kwamitin da zai tsara dabarun da za a bi wajen yi wa ma'aikata ƙarin albashi
- Shugaban ma'aikatan jihar, Elijah Evineme zai jagoranci kwamitin wanda ya kunshi kusoshin gwamnati da wakilan ƴan kwadago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi - Gwamnatin Kogi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Ododo ta kaddamar da kwamitin aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Kogi, Dr. Folashade Ayoade ya fitar ranar Laraba a Lokoja.
Dr Ayoade ya buƙaci mambobin kwamitin su sauke nauyin da aka dora musu domin fara biyan ma'aikata sabon albashin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin albashi ya sha alwashin aikin tukuru
Shugaban ma'aikatan gwamnatin a jihar Kogi, Mista Elijah Evineme, shi aka naɗa a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin.
Da yake jawabi bayan rantsar da su, Elijah Evineme ya tabbatar wa al'umma cewa kwamitin zai yi aiki tukuru don cika aikin da aka ɗora masa, Punch ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa shi da sauran ƴan kwamitin ba za su ba ma'aikata kunya ba dangane da aikin da aka sa su domin fara biyan sabon albashi mafi ƙaranci.
Kogi: Waɗanda aka sa a kwamitin albashi
Kwamitin ya kunshi manyan ƙusoshin gwamnatin Kogi da suka haɗa da kwamishinan kudi, Asiwaju Idris Asiru da kwamishinan ƙananan hukumomi Alhaji Ozigi Deedat.
Sauran ƴan kwamitin su ne kwamishinan yaɗa labarai, Kingsley Fanwo, Akanta-Janar Hajia Habitat Onumoko da Audita Janar na jihar Kogi,Yakubu Okala.
Sai kuma mai binciken kudin kananan hukumomi, Isiaka Yakubu, mai ba gwamna shawara kan harkokin ma'aikata, Kwamared Onuh Edoka da wakilan ƴan kwadago.
Gwamna Bago ya kafa sharaɗin biyan sabon albashi
A wani labarin kuma gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take wajen fara biyan ma'aikata albashi na N70,000.
Gwamnatin Neja ta bayyana cewa za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin da zarar wasu abubuwa da ta tasa a gaba sun kammala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng