"Za Ku Je Gidan Yari": Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi kan kin Biyan Albashin N70,000

"Za Ku Je Gidan Yari": Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi kan kin Biyan Albashin N70,000

  • Gwamnatin Tarayya ya yi barazanar tasa keyar duk ma'aikatu zuwa gidan yari da suka gaza biyan mafi ƙarancin albashi
  • Gwamnatin ta ce biyan mafi ƙarancin albashi N70,000 shi zai rage radadin da al'umma ke ciki na mawuyacin hali
  • Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da mafi ƙarancin albashin N70,000 a matsayin doka a fadin kasar baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta gargadi ma'aikatu masu zaman kansu kan biyan mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin ta ce ba za ta amince da biyan ma'aikaci kasa da N70,000 ba a ma'aikatun gwamnati ko masu zaman kansu.

Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki kan rashin biyan mafi ƙarancin albashi
Gwamnatin Tarayya ta gargadi ma'aikatu kan kin biyan mafi ƙarancin albashin N70,000. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Albashin N70,000: Gwamnati za ta dauki mataki

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, an bayyana yawan tirelolin shinkafar da shugaba Tinubu ya turo Kano

Babban sakatare a ma'aikatar kwadago, Alhaji Ismaila Abubakar shi ya bayyana haka a jiya Laraba 18 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ismaila ya ce tilasta biyan mafi ƙarancin albashin ne kadai zai rage yawan radadin halin da ake ciki a kasar.

Daraktan kwadago da albashi, John Nyamali shi ya wakilce shi inda ya fadi muhimmancin biyan mafi ƙarancin albashin, Tribune ta ruwaito.

Gwamnatin Tinubu ta yi gargadi kan albashin N70,000

"Mafi ƙarancin albashi yanzu ya zama doka, saboda duk ma'aikatu da ba za su biya ba za su fuskanci hukunci."
"Duk ma'aikatu masu zaman kansu su tabbatar sun biya mafi ƙarancin albashi N70,000 kuma ya kamata ya zama bayan cire haraji."
"Yanzu doka ce duk wanda ya saɓa biyan N70,000 zai fuskanci zuwa gidan yari dole kowane ma'aikaci ya samu albashi mai tsoka."

Kara karanta wannan

Ana murnar kisan ubangidan Bello Turji, gwamna ya ƙara tona badaƙalar ministan Tinubu

- John Nyamali

Gwamna Bago ya shirya biyan albashin N70,000

Kun ji cewa Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take wajen fara biyan ma'aikata albashi N70,000.

Gwamnatin Neja ta bayyana cewa za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin da da zarar wasu abubuwa sun kammala.

Umaru Bago ya bayyana haka ne a yayin wani taron da kungiyar ma'aikatan lafiya ta MHWUN ta shirya a birnin Minna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.