Zaben Edo: Babban Hafsan Tsaro Ya Yi Gargadi yayin da Ake Shirin Fara Kada Kuri'a

Zaben Edo: Babban Hafsan Tsaro Ya Yi Gargadi yayin da Ake Shirin Fara Kada Kuri'a

  • Babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa ya ja kunnen masu shirin yin rikici a zaɓen gwamnan jihar Edo
  • Janar Christopher ya yi gargaɗin cewa duk wani mai shirin kawo hargitsi a lokacin zaɓen jihar zai ɗanɗani kuɗarsa
  • Gargaɗin babban hafsan tsaron na zuwa ne da ake shirin gudanar da zaɓen gwamnan a ranar Asabar, 21 ga Satumba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, ya yi magana kan zaɓen gwamnan jihar Edo da ke tafe.

Babban hafsan tsaron ya garɗaɗi duk wasu masu shirin kawo rikici a zaɓen da su shiga taitayinsu.

Janar Musa ya yi gargadi kan zaben gwamnan Edo
Janar Christopher Musa ya aika da sakon gargadi kan zaben Edo Hoto: Defence Headquarters HQ
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Christopher Musa ya yi gargaɗin ne yayin wata ganawa da yayi da manyan jami'an sojoji a birnin Benin, babban birnin jihar Edo a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ambaliyar ruwa, Gwamna Zulum ya gargadi sarakunan Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane gargaɗi hafsan tsaro ya yi a Edo?

Babban hafsan tsaron ya bayyana cewa duk wanda ya yi yunƙurin kawo cikas a zaɓen zai ɗanɗani kuɗarsa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Abin da na kawo daga Abuja shi ne zaman lafiya da kuma tabbatar da cewa za mu yi aiki bisa ƙwarewa a lokacin zaɓen."
"Dole ne a gudanar da zaɓen cikin adalci da sahihanci, hakan na nuni da cewa duk wani mai wata niyya ta daban wacce ba ta yin zaɓe cikin kwanciyar hankali ba, tabbas zai ɗanɗani kuɗarsa."
"Ina kuma son na nanata, hukumomin tsaro ba za su amince wasu mutane su ɗauki makamai ba."

- Janar Christopher Musa

Ya gargaɗi jami’an tsaro na cikin gida da ƴan banga da su nesanta kansu da zaɓen, yana mai cewa ba su daga cikin hukumomin da aka ɗorawa alhakin samar da tsaro a lokacin zaɓen.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki, sun yi garkuwa da wani shugaban al'umma

Karanta wasu labaran kan zaɓen Edo

PDP ta gindaya sharuɗa kan zaɓen Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo na ranar 21 ga Satumba, 2024, Asue Ighodalo ya gindawa gwamnatin tarayya da 'yan sanda sharuda.

Mista Ighodalo ya ce jam'iyyar PDP a Edo ba za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba har sai gwamnati da 'yan sanda sun cika dukkanin sharuddansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng