Sarki Mai Martaba a Arewa Ya Kare Shugaba Tinubu, Ya Faɗi Namijin Kokarin da Yake Yi

Sarki Mai Martaba a Arewa Ya Kare Shugaba Tinubu, Ya Faɗi Namijin Kokarin da Yake Yi

  • Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu na iya bakin ƙoƙarinsa amma ƴan Najeriya ba su gane ba
  • Mai martaba sarkin ya ce gwamnatocin da suka gabata sun talauta Najeriya yayin da Tinubu ke ƙoƙarin kwato kudin da suka sace
  • Alhaji Umar Farouk ya faɗi haka ne a wurin taron wayar ɗa kan jama'a kan tallafin da gwamnatin Tinubu ke bayarwa na rage raɗaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Mai Martaba Sarkin Minna a jihar Neja, Alhaji Umar Farouk Bahago ya ce da yawan ƴan Najeriya ba su fahimci ƙoƙarin da Bola Tinubu ke yi ba.

Sarkin ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙarin kwato maƙudan kuɗin da aka sace a gwamnatocin da suka shuɗe amma galibin mutane ba su sani ba.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba a APC ya caccaki Tinubu, ya fadi yadda Abacha ya yi masa fintinkau

Shugaba Bola Tinubu.
Sarkin Minna ya ce Bola Tinubu yana namijin kokari wajen ceto Najeriya daga cin hanci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya faɗi haka ne a wurin taron wayar da kan ‘yan kasa kan shirye-shiryen tallafin da gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro wanda ofishin ministan yada labarai ya shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta ce Hadinin Minna, Alhaji Maikudi Achaza, shi ne ya wakilci mai martaba sarki a taron wanda ya gudana a babban birnin jihar Neja.

Wane namijin ƙoƙari Tinubu ke yi?

Alhaji Umar Farouk ya kare shugaban ƙasa Tinubu da cewa yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen ceto Najeriya daga cin hanci da rashawar shugabannin da suka wuce.

Ya ce galibin ƴan Najeriya ba su san tallafin da gwamnatin Tinubu ta ɓullo da su ba saboda masu magana da yawun gwamna ba su wayar da kan mutane a harsunan da suke ji.

Sarkin Minna ba gwamnatin Tinubu shawara

A rahoton Guardian, Sarkin Minna ya ce:

"An sace makudan kudade a gwamnatocin da suka shude wanda gwamnati mai ci ke kokarin kwatowa amma mutane da yawa ba su ma san inda aka dosa ba.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Aminu Ado Bayero ya jajantawa mutanen Borno, ya yi addu'a

"Tun da aka tuge tallafin man fetur, gwamnati ta zo da tsare-tsare da dama don ragewa mutane raɗaɗi. Ya kamata gwamnati ta riƙa wayar da kan jama'a da harshen da suke ji."

An ba Tinubu mafita kan tsadar kayayyaki

A wani rahoton kuma Oba na Iwoland, Abdulrosheed Akanbi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya samar da hukumar kayyade farashin kaya a kasar.

Akanbi ya ce wannan mataki ne kadai zai dakile hauhawan farashin da wasu masu hadama ke yi a duk lokacin da suka ga dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262