Ambaliyar Ruwa: Remi Tinubu Ta Tallafawa Al'ummar Jihar Borno da N500m

Ambaliyar Ruwa: Remi Tinubu Ta Tallafawa Al'ummar Jihar Borno da N500m

  • Uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kai ziyarar jaje a Maiduguri domin nuna alhini kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Borno
  • Oluremi Tinubu da ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban ƙasa, ta ba da gudunmawar N500m domin tallafawa mutanen da lamarin ya shafa
  • Ta jajantawa Gwamna Babagana Umara Zulum da al'ummar jihar Borno kan ambaliyar ruwan da ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Uwargidan Shugaba Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu, ta nuna alhininta kan ambaliyar ruwan da ta auku a Borno.

Remi Tinubu ta ba da gudunmawar N500m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: 'Yan siyasa sun zabura, majalisar wakilai ta tallafa da N100m

Remi Tinubu ba da tallafi a Borno
Remi Tinubu ta ba da N500m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno Hoto: Senator Oluremi Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa uwargidan shugaban ƙasan ta ba da gudunmawar ne yayin ziyayar jaje a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Remi Tinubu ta ba da gudunmawa a Borno

Remi Tinubu wacce ta samu wakilcin uwargidan mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, ta nuna damuwa kan ambaliyar ruwan wacce ta bayyana a matsayin ƙaddara ce daga Allah.

Ta jajantawa Gwamna Babagana Umara Zulum da al'ummar Borno inda ta bayyana cewa Allah ne kaɗai zai maida musu abin da suka yi asara, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

A nasa ɓangaren, Gwamna Zulum ya godewa tawagar bisa ba da gudunmawar da za ta taimaka wajen tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.

Tawagar wacce ta ƙunshi matan manyan masu riƙe da muƙamai a gwamnati, ta kuma kai ziyarar jaje ga Shehun Borno, Dr. Abubakar Ibn Garbai Al-amin Elkanemi.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Aminu Ado Bayero ya jajantawa mutanen Borno, ya yi addu'a

Karanta wasu labaran kan ambaliyar ruwa a Borno

Gwamnan Borno ya gargaɗi sarakuna

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi masu riƙe da sarautun gargajiya.

Gwamna Zulum ya gargaɗi sarakunan ne kan illolin da ke tattare da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a cikin yankunansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng