Badaƙalar N80bn: Yahaya Bello Ya Faɗi Yadda Ta Kaya bayan Ya Miƙa Ƙansa ga EFCC
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya baro ofishin EFCC salin-alin ba tare da jami'ai sun titsiye shi da tambayoyi ba
- Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Ohiare Michael ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Laraba
- Hakan na zuwa ne bayan Yahaya Bello ya amsa gayyatar EFCC kan zargin wawure kuɗin talakawa a lokacin da yake mulkin Kogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya baro ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da ke Abuja jim kaɗan bayan ya mika kansa.
A yau Laraba, 18 ga watan Satumba, 2024, Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta masa kan zargin wawure kuɗi sama da N80bn daga baitul malin jihar Kogi.
Leadership ta ce hakan na zuwa ne bayan wasan ɓuya na tsawon watanni tsakanin jami’an hukumar yaki da satar dukiyar al’umma da tsohon gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda EFCC ke neman Yahaya Bello
Idan ba ku manta ba, EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo bayan ya gaza mutunta gayatar da hukumar ta yi masa da kuma ƙin halartar zaman kotu.
Sai dai a yau Laraba, Yahaya Bello tare da magajinsa, Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, suka je hedkwatar EFCC da ke birnin tarayya Abuja.
A cewar tsohon gwamnan ya je ofishin EFCC ne domin amsa gayyatar da aka masa da kuma wanke kansa daga zargin satar kuɗin al'umma.
Yahaya Bello ya magantu bayan baro EFCC
Amma bayan haka, Yahaya Bello, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Ohiare Michael, ya ce tuni ya bar hedkwatar EFCC.
Ya ce ya baro ofishin hukumar EFCC ba tare da an bincike shi ba bayan jami'an hukumar sun ba shi izinin ya tafi, rahoton Channels tv.
“Hukumar EFCC ba ta titsiye shi da wasu tambayoyi ba, jami’ai suka ba shi izinin ya tafi, ba mu san abin da hakan ke nufi ba tukuna."
"A yanzu dai Mai Girma Alhaji Yahaya Bello ya bar ofishin EFCC, inda ya samu rakiyar gwamnan jihar Kogi Alhaji Ahmed Usman Ododo."
- Ohiare Michael.
Hukumar EFCC ta mayar da martani
A wani rahoton kun ji cewa hukumar EFCC ta yi martani kan rade-radin cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya mika kansa gare ta.
Hukumar ta ce har yanzu tana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo kan zargin karkatar da makudan kudi har N80.2bn.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng