Dattawan Zamfara Sun Ba Gwamna Dauda Shawara kan Matawalle
- Wata ƙungiyar dattawan Zamfara ta ba gwamnan jihar shawara kan abin da ya kamata yafi maida hankali a kansa a mulki
- Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Dauda Lawal da ya ba da fifiko wajen sauke nauyin da ke kansa maimakon sukar Bello Matawalle
- A cewar ƙungiyar ƙoƙarin ɓata sunan tsohon gwamnan ta hanyar zarginsa da cin hanci da rashin iya mulki abu ne da bai dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƙungiyar dattawan Zamfara ta Zamfara Elders Support for Peace and Development, ta yi kira da babbar murya ga gwamnan jihar, Dauda Lawal.
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Dauda da mayar da hankali wajen sauke nauyin da ke kansa maimakon sukar ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Wace shawara aka ba gwamnan Zamfara
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnan da ya mayar da hankali wajen samar da haɗin kai, kawo ci gaba maimakon ƙoƙarin kawo rarrabuwar kai ta fannin siyasa, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar dattawan ta yi martani ne kan kalaman da gwamnan ya yi kwanan nan, waɗanda ta bayyana a matsayin ƙoƙarin kawar da hankalin jama'a kan nasarorin da ake samu a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga a jihar.
Shugaban ƙungiyar Honorabul Aliyu Mammani Kaura ya bayyana cewa zargin cin hanci da rashin iya mulki da ake yi wa Matawalle ko kaɗan bai dace ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ƙungiya ta caccaki Gwamna Dauda
"Mu a wajenmu, lokacin mulkin Matawalle ya fi zama na gaskiya, mai amfani da samun zaman lafiya da tsaro ga mutanen Zamfara fiye da wannan gwamnatin mai ci yanzu."
"Yanzu mutanenmu na fama da rashin shugabanci mai kyau, ƙaruwar matsalar tsaro rashin ababen more rayuwa da lalata tattalin arziƙin Zamfara saboda gwamnan ya daina yin aikin da ke wuyansa."
"Kusan koda yaushe yana Abuja ko ba shi a ƙasar ba tare da yin abin a zo a gani da mutanen jihar za su amfana da shi ba."
- Honarabul Aliyu Mammani Kaura
Gwamna Dauda ya ba da tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 ga iyalan mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da su a jihar.
Mataimakin gwamnan Zamfara, Mani Mummuni, wanda ya yi magana a madadin gwamnan a ranar Talata, 17 ga watan Satumban 2024 ya sanar da ba da gudunmawar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng