'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki, Sun Yi Garkuwa da Wani Shugaban Al'umma
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ƙauyen Abatete, High Chief Ezebinobi Ezeigbo a jihar Anambra ranar Talata
- Rahoto ya nuna lamarin ya auku ne jim kaɗan bayan Gwamna ya rantsar da sabon kwamishinan yaɗa labarai, Dr Law Mefor
- Jami'an hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Anambra, Ikenga Tochukwu ya ce ba shi da masaniya game da sabon harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Wasu ƴan bindiga da suka kai kimanin biyar sun yi awon gaba da shugaban ƙauyen Abatete da ke ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.
Ƴan bindigar waɗanda ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da jagoran al'ummar Abatete, High Chief Ezebinobi Ezeigbo ranar Talata da ta gabata.
Vanguard ta gano cewa lamarin ya auku ne sa'o'i kaɗan bayan Gwamna Charles Soludo ya rantsar da ɗaya daga cikin ƴan asalin kauyen a matsayin kwamishinan yaɗa labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa a ranar Talata, Gwamna Soludo ya rantsar da Dr. Law Mefor a matsayin wanda zai maye gurbin kwamishinan yaɗa labarai da ya kora.
Yadda ƴan bindiga suka sace mutumin
Wata majiya daga kauyen da ta nemi a ɓoye bayananta, ta ce masu garkuwan sun bi sawun Ezeigbo tun daga Awka, inda ya halarci bikin rantsar da Mefor.
"Masu garkuwar sun biyo shi a motarsu a lokacin da yake komawa gida da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Talata, 17 ga Satumba, 2024, bayan rantsar da sabon kwamishinan yada labarai."
"Da zuwa kofar gidansa maharan suka fito suka kewaye shi da bindiga, suka umarci ya fito daga motarsa ya shiga ta su, ɗaya daga cikinsu kuma ya hau motarsa.
"A lokacin da suke ƙoƙarin tafiya ne sai wanda ya ɗauko motarsa ya faɗa cikin kwata, cikin hanzari ya bar motar nan ya shiga ta su, sannan suka tsere," in ji majiyar.
Ƴan sanda sun samu labarin harin?
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Anambra, SP Ikenga Tochukwu, ya ce ba shi da wani bayani game da lamarin, in ji Punch.
Martanin kakakin ƴan sanda a lokacin da aka tuntuɓe shi ya nuna ba ya son magana kan lamarin, ya ƙalubalanci ƴan jarida da cewa ba su da aiki sai neman bayani kan aikata laifuka.
Yan bindiga sun farmaki coci a Kaduna
Kuna da labarin ƴan bindiga sun shiga coci guda biyu, sun kashe mutane a garin Bakinpah-Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace mutane 30 ciki har da malamin coci a harin da suka kai ranar Lahadi da ta gabata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng