Yahaya Bello: EFCC Ta Bayyana Yadda Tsohon Gwamna Ya Shigo Hannunta
- Tsohon gwamnan jihar Kogi ya shiga hannun jami'an hukumar EFCC bayan kwashe lokaci mai tsawo suna wasan ɓuya
- Majiyoyi a hedkwatar hukumar sun bayyana cewa jami'an EFCC ne suka cafke Yahaya Bello ba amsa gayyatar hukumar ya yi ba
- Tun da farko dai tsohon gwamnan ya nuna cewa ya amsa gayyatar hukumar EFCC kan zargin da take yi masa na karkatar da N80.2bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yana tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
Tsohon gwamnan na Kogi yana tsare ne a hedkwatar hukumar da ke babban birnin tarayya Abuja.
Yadda Yahaya Bello ya shiga hannun EFCC
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ingantattun majiyoyi da ke hedkwatar EFCC sun bayyana cewa an cafke Yahaya Bello ne a wani samame da aka kai cikin tsakar dare a Lokoja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta bayyana cewa jami'an hukumar EFCC ne suka bi sawun tsohon gwamnan sannan suka cafke shi a birnin Lokoja.
"Yanzu haka tsohon gwamnan jihar Kogi yana tsare a hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja."
"An kama shi ne a Lokoja bayan jami'ai sun bi sawunsa sannan suka cafke shi a cikin tsakar dare."
- Wata majiya
Tun da farko dai, wata sanarwa daga daraktan yaɗa labaran tsohon gwamnan, Michael Ohiare ta bayyana cewa Yahaya Bello ya amsa gayyatar EFCC.
Karanta wasu labaran kan Yahaya Bello
- Yahaya Bello: Tsohon gwamna ya saduda, ya amsa gayyatar EFCC
- EFCC ta shirya cafke tsohon gwamnan APC, ta fadi matakan da ta dauka
- Shari'ar EFCC: Kotu ta lalata shirin Yahaya Bello, ta bukaci ya gurfana gabanta
Yahaya Bello ya nemi buƙata a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sake gabatar da buƙata a gaban babbar kotun tarayya.
Yahaya Bello ya buƙaci babbar kotun da ta ɗage ci gaba da sauraron shari'ar da hukumar EFCC ta shigar a kansa har sai baba ta gani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng