Man Fetur: An Sake Samun Rikici tsakanin Dangote da Kamfanin NNPCL

Man Fetur: An Sake Samun Rikici tsakanin Dangote da Kamfanin NNPCL

  • An sake samun alkaluma mabanbanta kan man fetur da kamfanin mai na NNPCL ya dauka daga matatar Dangote
  • Matatar Dangote ta ce ta ba kamfanin NNPCL man fetur har lita miliyan 111 tun da ta fara ba kamfanin mai a ranar Lahadi
  • Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa matatar Dangote za ta iya fitar da tataccen mai ne da bai wuce lita miliyan 16.8

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - An samu bayanai mabanbanta kan adadin man fetur da matatar Dangote ta ba kamfanin NNPCL.

Matatar Dangote ta ce ta cigaba da loda tataccen man fetur ga kamfanin NNPCL bayan an fara lodin a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

NNPCL ya fadi lokacin da matatar man gwamnati za ta fara aiki gadan gadan

Matatar Dangote
Matatar Dangote ta musa maganar NNPCL. Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'in yada labarai a matatar Dangote, Anthony Chiejina ya bayyana adadin da suka ba kamfanin NNPCL.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar NNPCL kan man matatar Dangote

Bayan fara dibar man fetur a matatar Dangote, kamfanin NNPCL ya ce ya loda mai lita miliyan 16.8.

NNPCL ya ce an samu karanci a kan adadin farko na lita miliyan 25 da matatar Dangote za ta samar.

Matatar Dangote ta musa maganar NNPCL

Matatar Dangote ta fitar da rahoto a kan man fetur da ta fitar ga NNPCL inda ta ce a yanzu ta ba kamfanin mai lita miliyan 111.

Haka zalika, jami'in matatar Dangote, Anthony Chiejina ya ce sun cigaba da loda mai ga kamfanin NNPCL tun ranar Lahadi.

Me NNPCL zai ce kan matatar Dangote?

Biyo bayan sabon bayanin da matatar Dangote ta fitar manema labarai sun nemi jin ta bakin NNPCL.

Kara karanta wannan

Rikicin farashi: Yan kasuwa sun gaza samun man Dangote daga NNPCL

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton kamfanin NNPCL bai amsa sakon da aka tura masa ba.

An samu sabani tsakanin Dangote da NNPCL

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da yan Najeriya ke cigaba da tsammanin sauki a farashin fetur an samu sabani tsakanin NNPCL da matatar Dangote.

An samu bayanai mabanbanta kan yadda cinikin man fetur ya kullu tsakaninsu inda suka fitar da sanarwa mai karo da juna kan yadda suka kulla ciniki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng