Kotu ta Dage Yanke Hukunci a Shari'ar Korar Shugaban APC, Ganduje daga Mukaminsa
- Babbar kotu da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta kara kwanaki kafin yanke hukunci kan karar da ke neman a kori Abdullahi Ganduje
- Jagora a APC da ya fito daga Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga na ganin bai da ce Dr. Ganduje ya jagoranci jam'iyyar ba saboda yankin da ya fito
- Zazzaga ya ce mukamin shugabancin APC a yanzu ya fada shiyyarsu, wanda hakan ya sa su mika damuwarsu zuwa babbar kotun tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta dage yanke hukunci kan shari'ar da ke neman a kori shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje daga mukaminsa.
Tun a baya, kotun ta sanya wannan rana a matsayin ranar hukunci kan dambarwar da ta ke kokarin hana Dr. Ganduje jagorancin jam'iyyar APC.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kotun ta sanya sabuwar ranar da za a yanke hukuncin ko Ganduje zai ci gaba da zama shugaban jam'iyyar APC na kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a yanke hukunci a shari'ar Ganduje?
Premium Times ta wallafa cewa babbar kotun tarayya ta ce za ta yanke hukunci kan dambarwar shugabancin jam'iyyar APC ta kasa a ranar 23 Satumba, 2024.
Tuni magatakardar kotun ya shaida wa bangaren wanda ake kara, Abdullahi Ganduje da masu karar jinkirin da aka samu kan shari'ar.
Su wanene ke son a tsige Abdullahi Ganduje?
Jigo a APC daga Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga ne ya shigar da kara ya na kalubalantar zaman Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyarsu.
Alhaji Zazzaga da sauran masu kara na ganin bai dace Ganduje ya jagorancin APC ba domin bai fito daga yankin Arewa ta Tsakiya ba, hakan ya sa su ka nemi kotu ta dakatar da shi.
An yi hasashen Ganduje zai bar APC
A baya mun ruwaito cewa wani malamin addinin kirista, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje zai tafi.
Wannan zai biyo bayan rikici da zai balle tsakanin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng