Daga Ƙarshe, An Bayyana Yawan Tirelolin Shinkafar da Shugaba Tinubu Ya Turo Kano
- Gwamnatin tarayya ta tura tallafin tirela 19 na shinkafa zuwa Ƙano domin a rabawa talakawa da ke cikin yunwa
- Maryam Shetima, ƴar kwamitin rabon tallafin abincin ce ta bayyana haka ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024
- Ta ce kwamitin ya gama tsare-tsaren da ya kamata domin tabbatar da kayan abincin sun isa hannun mabuƙata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu ta bai wa jihar Kano tallafin tireloli 19 na shinkafa a wani mataki na rage yunwa a tsakanin al'umma.
Ɗaya daga cikin ƴan kwamitin da gwamnati ta kafa domin sa ido kan yadda za a raba tallafin, Maryam Shetima ce ta bayyana haka ranar Litinin.
A wata hira da Arise tv, Maryam Shettima ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta aiko tirela 19 maƙare da buhunan shinkafa zuwa Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maryam Shetty da aka cire sunanta daga jerin ministoci gabanin majalisar dattawa ta tantance ta, ta tabbatar cewa kwamitin ya yi tsari yadda sakon zai isa ga talakawa.
Gwamnatin Tinubu ta ba Kano tirela 19
A rahoton da Premium Times ta tattara, Maryam ta ce:
"Tirela 19 na shinkafa aka ba Kano, ban da tabbacin adadin da aka tura sauran jihohi amma dai na san wannan somin taɓi ne. Ku duba an ba Kano tirela 19, nawa kuke tunanin za a turawa sauran jihohi 36."
Ta ba da tabbacin cewa bisa tsarin da kwamitin ya yi, wannan kayan tallafi za su isa ga talalakawa da marasa galihu a faɗin kananan hukumomin Kano.
Sai dai Maryam ba ta ce komai ba game da girman buhunan shinkafar, wanda zai iya zama kilo 10, 25 ko 50.
Jibrin ya koka kan karkatar da tallafi a Kano
A kwanakin baya mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya nuna damuwa kan yadda wasu ɗaiɗaiku ke karkatar da tallafin Bola Tinubu da aka turo Kano domin amfanin kansu.
Sanata Barau Jibirin, mai wakiltar Kano ta Arewa, shi ne shugaban kwamitin rabon kayan agaji na gwamnatin tarayya a Kano.
Yayin da take amsa tambaya game da yiwuwar karkatar da shinkafar, Maryam Shettima ta ba da tabbacin cewa mambobin kwamitin za su yi adalci wajen rabon.
Ta ce babu alfarma ko son zuciya, kwamitin zai yi bakin ƙoƙarinsa wajen raba kayan abincin ga mabukata ba tare da nuna banbancin jam'iyya ba.
Gwamnan Kano ya ba Borno tallafin N100m
A wani rahoton kuma gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kai tallafin Naira miliyan 100 ga al'ummar Maiduguri da ambaliyar ruwa ta rutsa da su.
Gwamnatin Kano ta bayar da tallafin ne bayan da ta kai ziyarar duba irin barnar da ambaliyar ta yi tare da jajantawa al'ummar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng