Ambaliyar Maiduguri: 'Yan Siyasa Sun Zabura, Majalisar Wakilai Ta Tallafa da N100m

Ambaliyar Maiduguri: 'Yan Siyasa Sun Zabura, Majalisar Wakilai Ta Tallafa da N100m

  • Majalisar wakilai ta bi sahun Sanatocin majalisar dattawa da yan siyasa a kasar nan wajen kai gudunmawa ga gwamnatin jihar Borno
  • Daidaikun jama'a da yan siyasa sun tashi haikan wajen mika tallafi ga gwamna Babagana Zulum domn taimakon wadanda ambaliya ta shafa
  • Tawagar majalisar wakilan, karkashin jagorancin Rt. Hon. Alhassan Doguwa ta yi takakkiya zuwa Maiduguri domin bayar da tallafinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Rt. Hon. Alhassan ya jagoranci tawagar wakilan zuwa Maiduguri domin jajanta wa gwamnan jihar da mutanensa.

Borno na karbar tawaga da manyan baki da ke kai ziyara domin jajanta wa kan afkuwar iftila'in ambaliya da ta shafi mutane sama da miliyan biyu a jihar.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Yan majalisar dattawa sun ziyarci Borno, sun mika tallafin N74m

Borno
Majalisar wakilai ta ba jihar Borno tallafin N100m Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

A sanarwar da majalisar ta wallafa a shafinta na Facebook, an bayyana cewa yan majalisar da su ka ziyarci Maiduguri sun wakilci shiyyoyin kasar nan shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan majalisar wakilai sun bayar da tallafi

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa yan majalisar wakilan kasar nan sun taimaka wa gwamnatin jihar Borno da Naira Miliyan 100 domin agaza wa jama'ar da ambaliya ta shafa cikin gaggawa.

A jawabinsa yayin mika tallafin, Rt. Hon. Ado Doguwa ya bayyana cewa dukkanin yan majalisar ne su ka hada tallafin.

Majalisa ta yi alkawarin magance ambaliya

Majalisar wakilan kasar nan ta yi alkawarin bayar da hadin kai wajen nemo hanyoyin magance ambaliya a fadin Najeriya.

Majalisar ta kuma jaddada jajenta ga Borno, tare da bayyana cewa ta na tare da jihar a wannan lokaci na bala'in ambaliya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bude wuta, an damke masu taimakon 'yan bindigan Arewa da makamai

Dantata ya ba da tallafin N1.5bn

A baya mun ruwaito cewa dattijon dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata ya bayar da tallafin Naira Biliyan 1.5 ga gwamnatin jihar Borno domin rage radadin iftila'in ambaliya ga mazauna Maiduguri.

Alhaji Dantata ya ja kunnen shugabannin kasar nan su nutsu, tare da sauke nauyin yan kasa da ya rataya a wuyansu, inda ya ce yan Najeriya na fama da mawuyacin halin tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.