Ambaliya: Yan Majalisar Dattawa Sun Ziyarci Borno, Sun Mika Tallafin N74m
- Majalisar dattawan kasar nan ta aika tawaga ta musamman zuwa Borno domin jajanta wa gwamna Babagana Zulum kan ambaliya
- Har yanzu jama'a na cikin mawuyacin hali bayan ruwa ya haura madatsar Alau, ya kuma mamaye gidaje, hanyoyi da sauran wurare
- A ziyarar da mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ya jagoranta, majalisar ta mika tallafin miliyoyin kusi domin taimakon jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - A ranar Talata ne tawagar yan majalisar dattawa ta ziyarci gidan gwamnatin jihar Borno domin jajanta wa jama'ar Maiduguri bisa mummunan iftila'in ambaliya.
Mataimakin shugaban majalisar, Barau I Jibrin ne ya jagoranci tawagar, inda ya bayyana cewa su na sane da girman iftila'in da mawuyacin halin da ya jefa jama'a.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau I Jibrin ya yi addua'ar Allah SWT ya gafarta wa wadanda su ka rasu da addu'ar marasa lafiya za su samu sauki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar dattawa ta ba Borno tallafin N74m
Yan majalisar dattawan kasar nan su 108 sun tattara N500, 000 kowanensu, inda aka mika jimullar Naira Miliyan 54 ga gwamna Babagana Zulum.
Mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ya bayar da tallafi na kashin kansa na Naira Miliyan 10, sannan sanatocin Arewa sun kara wata Naira Miliyan 10 a kudin tallafin.
Majalisa ta yi addua'a kan iftila'in ambaliya
Sanata Barau I Jibrin ya yi addu'ar Allah SWT ya taimaka wa jama'ar da su ka fada mawuyacin hali sakamakon albaliya a Maiduguri.
A ziyarar da su ka kai Borno, tawagar yan majalisar ta biya gidan Sanata Baba Kaka Garbai tare da yi masa ta'aziyya bisa rasuwar mahaifiyarsa.
Shugaban majalisa ya jajanta kan ambaliyar Borno
A baya kun ji cewa shugaban majalisar dattawan kasar nan, Sanata Godswill Akpabio ya mika jaje da ta'aziyya ga jama'ar jihar Borno bisa ambaliya da ta daidata mazauna Maiduguri.
Sanatan ya bayyana cewa majalisa za ta yi duk abin da ya dace domin ganin an tallafa wa mutanen da su ka fada mawuyacin hali, domin a saukaka masu halin da su ke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng