Yahaya Bello: Tsohon Gwamna Ya Saduda Ya Amsa Gayyatar EFCC

Yahaya Bello: Tsohon Gwamna Ya Saduda Ya Amsa Gayyatar EFCC

  • Daga ƙarshe tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta yi masa
  • Alhaji Yahaya Bello ya amsa gayyatar ne bayan ya kwashe dogon lokaci yana wasan ɓuya da jami'an hukumar EFCC a Najeriya
  • EFCC dai a kwanakin baya ta ayyana tsohon gwamnan a matsayin wanda take mena ruwa a jallo bayan ya ƙi amsa gayyatarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sanar da shirinsa na amsar gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa.

Hukumar EFCC dai ta ayyana tsohon gwamnan a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin karkatar da N80.2bn a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba a APC ya caccaki Tinubu, ya fadi yadda Abacha ya yi masa fintinkau

Yahaya Bello ya amsa gayyatar EFCC
Yahaya Bello ya amince zai amsa gayyatar EFCC Hoto: Alhaji Yahaya Bello, EFCC
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labaran tsohon gwamnan, Ohiare Michael, ya sanar da hakan a ranar Laraba a cikin wata sanarwa wacce aka sanya a shafin Facebook na Yahaya Bello.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Yahaya Bello ya amsa gayyatar EFCC?

A cewar sanarwar tsohon gwamnan ya cimma matsayar ne bayan ya tattauna da iyalansa, lauyoyinsa da abokanansa na siyasa.

A cewarsa, tsohon gwamnan ya nemi kawai a kare haƙƙinsa na ɗan Adam ne domin tabbatar da bin doka da oda, inda ya ƙara da cewa shi mai mutunta doka ne.

"Ƙarar tana gaban kotu sannan Yahaya Bello yana samun wakilcin lauyoyinsa a kowane zama."
"Yana da muhimmanci a yanzu tsohon gwamnan ya amsa gayyatar EFCC domin ya wanke kansa saboda ba ya da wani abin da zai ɓoye."
"Tsohon gwamnan ya yarda da ƙoƙarin da gwamnatin shugaban ƙasa Tinubu ke yi na farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya tare da goyon bayan yaƙi da cin hanci a ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Gwamna ya kori kwamishinansa bayan shekara 3, an gano dalilinsa

- Michael Ohiare

Yahaya Bello ya samu rakiya

Michael Ohiare ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya samu rakiyar wasu manya-manyan ƴan Najeriya zuwa ofishin EFCC.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a bayyana yadda ganawar ta su ta kasance a nan gaba.

EFCC na shirin cafke Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta yi magana kan cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Hukumar EFCC ta ce tana aiki da hukumomi na cikin gida da na waje domin ganin an gurfanar da tsohon gwamnan gaban kuliya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng