Ana Batun Kara Haraji, Gwamnoni 20 Sun Runtumo Bashin Naira Biliyan 446

Ana Batun Kara Haraji, Gwamnoni 20 Sun Runtumo Bashin Naira Biliyan 446

  • Wani rahoto daga bayanan aiwatar da kasafin kudi na jihohin Najeriya ya nuna cewa gwamnani 20 sun karbo bashin N446bn
  • Rahoton ya nuna gwamnatocin jihohin sun karbo wannan tulin bashin ne duk da cewa sun samu karin kudi da 40% daga tarayya
  • Wannan na zuwa ne yayin da masana ke gargadin cewa yawan karbo bashi na da tasiri ga gudanar da ayyukan jama'a da na kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gwamnatocin jihohi 29 sun batar da kusan kashi 80.7 na kudaden harajin cikin gida da suke taraya a wajen biyan basussukan da suka karbo.

An ce gwamnatocin sun biya wadannan basussukan ne a watanni shida na farkon shekarar 2024 wanda masana suka nuna damuwa a kai.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Ya na murna ya tsere daga kurkuku, jami'an tsaro sun cafke shi

Rahoton yadda gwamnoni 20 suka karbo bashin Naira biliyan 446
Yadda gwamnoni 20 suka karbo bashin Naira biliyan 446. Hoto: @NGW_Forum
Asali: Twitter

Gwamnoni 20 sun ciyo bashin kudi

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa jihohin kasar nan na fuskantar matsalar kudi inda hakan ta tilasta gwamnoni 20 ciyo bashin Naira biliyan 446.29.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa gwamnonin sun karbo wannan bashi ne duk da cewa sun samu karin kaso 40 daga asusun tarayya.

An ce an tattara wannan bayani ne daga shafin fitar da rahoton aiwatar da kasafi na kowacce jiha wanda cibiyar bin diddiki ta BudgIT ta ke marawa baya.

Ana shirya wannan rahoton ne bayan watanni uku kuma ana fitar da shi makonni hudu bayan karshen kowane zango na shekara.

Tasirin bashin ga tattalin jihohi

Masana na ganin karbo irin wannan bashi na da tasiri wajen raunana gudanar da kasafin kudi, saboda yawancin kudaden ayyukan jama'a kan tafi wajen biyan basussukan.

Kara karanta wannan

Rahoton NBS: Google, Facebook da sauran kamfanonin waje sun biya harajin N2.55tn ga Najeriya

Rahoton ya kuma nuna irin matsalolin da gwamnoni ke fuskanta wajen tafiyar da basussukan da suka gada daga gwamnatocin baya da kuma biyan bukatun jama'arsu.

‘Yan Najeriya dai suna cike da tsammanin samun romon dimokuradiyya bayan da jihohi suka samu karin kaso 40 daga gwamnatin tarayya, wanda ake ganin zai wadaci bukatun jama'a.

Gwamnatin Najeriya za ta kara haraji?

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta ce ta kammala tsara daftarin karin harajin VAT wanda za ta gabatarwa majalisar tarayyar kasar nan gaba kadan.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa na musamman domin gyara kasafi da tattalin arzikin kasar ne ya bayyana hakan, inda ya ce harajin 7.5% da ake biya yanzu ya yi kadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.