Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 20 da Aka Sace
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun ƴan bindigan da suka addabi mutanen jihar Kaduna a Arewa
- Sojojin sun hallaka ƴan bindiga mutum huɗu a wani samame da suka kai a ƙananan hukumomi guda biyu na jihar
- Jami'an tsaron Najeriyan sun kuma kuɓutar da wasu mutane 20 da miyagun suka yi garkuwa da su zuwa cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Dakarun sojoji sun samu nasarar kashe ƴan bindiga mutum huɗu a jihar Kaduna.
Sojojin sun kuma samu nasarar kuɓutar da wasu mutane 20 da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka kashe ƴan bindiga
Samuel Aruwan ya bayyana cewa dakarun Operation Forest Sanity sun kai samame na musamman a garin Alawa da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun hango wasu ƴan bindiga da suka addabi garin Kwaga, inda bayan wani musayar wuta suka yi nasarar hallaka ƴan bindigar guda biyu.
Dakarun sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, jigida guda uku, babura guda uku, da rediyon Baofeng guda ɗaya.
Hakazalika, sashe na shida na rundunar Operation Whirl Punch sun gudanar da sintiri a kusa da ƙauyen Nakwakina, cikin ƙaramar hukumar Giwa.
Bayan samun sahihan bayanan sirri, sojojin sun yi ƙwanton bauna a hanyar da ake zargin ƴan ta'adda na wucewa.
Wannan artabun ya yi sanadiyyar kashe ƴan ta'adda biyu, yayin da wasu suka gudu da ɗauke raunukan harbin bindiga. Sojojin sun ƙwato babura biyu, adda ɗaya da wayar hannu daya.
Sojoji sun kuɓutar da mutane
Bugu da ƙari, sashe na uku na rundunar Operation Whirl Punch da aka girke a hanyar Kwaga-Falwaya a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, sun tare wasu ƴan bindiga da suka yi garkuwa da mutane a kusa da ƙauyen Falwaya.
Ƴan bindigan sun gudu bayan ganin sojojin, inda suka kuɓutar da mutane 20 da aka yi garkuwa da su tare da sada su da iyalansu.
Sojoji sun cancanci yabo
Abdulmalik Kuriga mazaunin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarorin da sojojin suka samu abin a yaba ne.
Ya bayyana cewa a yanzu wurarensu ana samun ci gaba ta fannin tsaro sosai.
"Eh gaskiya wannan abin a yaba ne sosai, jami'an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu kuma al'amura na yin kyau yanzu a yankunan mu domin mun samu mun yi noma."
- Abdulmalik Kuriga
Ƴan bindiga sun hallaka sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ma'aikatan kamfanin gine-gine a hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe mutane bakwai ciki har da sojoji uku waɗanda suke yi wa injiniyoyi ƴan ƙasashen waje rakiya.
Asali: Legit.ng