Gaskiya da Gaskiya: CBN Ya Fadi Illar da Za a Fuskanta kan Cire Tallafin Man Fetur
- Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da rahoto a kan matsalar da za a iya fuskanta kan cire tallafin fetur da gwamnati ta yi
- CBN ya kuma yi hasashen cewa za a fuskanci barazanar tattalin arziki kan yadda Najeriya ke kashe kudi a kan biyan bashi
- Tun farkon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya furta cewa ya cire tallafin man fetur domin daidaita tattalin arzikin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi bayani kan illar da cire tallafin man fetur za ta iya haifarwa a Najeriya.
Bankin CBN ya ce za a iya fuskantar barazana da ta shafi tattalin arzikin Najeriya kan cire tallafin man fetur.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Bankin CBN ya fitar da rahoto ne yayin wani taron da ya shafi tsare tsaren kudi na shekarun 2024/2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Illar cire tallafin man fetur a Najeriya
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce akwai barazana ga tattalin Najeriya kan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
CBN ya ce barazanar za ta iya kawo ci baya sosai ga haɓakar asusun ajiyar wajen Najeriya a shekarun 2024 zuwa 2025.
The Cable ta ce Bankin ya kara da cewa yawan cire kudi da ake yi a Najeriya domin biyan bashi zai iya zama barazana ga tattalin arzikin kasar.
Najeriya: Abin da zai yi tasiri ga tattali
Bankin CBN ya yi hasashen cewa matsalar harkar makamashi da ake fuskanta saboda yaƙin Ukraniya da Rasha zai iya kawo ci baya ga Najeriya.
Haka zalika bankin ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro na cikin abubuwan da ake hasashen za su iya zama barazana ga tattalin Najeriya.
Yan Najeriya dai na fama da matsalar tattalin arziki kuma sun zuba ido ga gwamnati domin kawo tsare tsaren da za su kawo saukin rayuwa.
Atiku ya yi magana kan tallafin mai
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda Bola Ahmed Tinubu ya ke jagorantar Najeriya.
Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar ya ce akwai lauje cikin naɗi kan yadda Bola Tinubu ya gaza yi wa ƴan kasa bayani kan lamarin tallafin man fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng