Shugaba Tinubu Ya Samar da Hukuma kan Shigo da Makamai Ta Haramtacciyar Hanya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa hukumar safarar makamai zuwa cikin kasar nan ba bisa ka'ida ba
- Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya tabbatar da haka a wani taro kan hana shigo da makamai Afrika
- Mal. Ribadu ya bayyana cewa amince wa da kafa hukumar zai taka muhimmiyar rawa wajen kakkabe safarar makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da samar da hukumar da za ta rika sanya idanu kan safarar makamai zuwa cikin kasar nan.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka a wani taro kan yadda za a hana shigo da makamai Yammacin Afrika.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Mashawarcin shugaban, ya samu wakilcin daraktan harkokin waje na ofishin NSA, Ambasada Ibrahim Babani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin kafa hukumar hana safarar da makamai
Jaridar Guardian ta wallafa cewa shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar yaki da shigo da makamai kasar nan saboda kakkabe ta'addanci.
Mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka, inda ya ce kafa hukumar wani muhimmin ci gaba ne ga gwamnatinsu.
Safarar da makamai: Ana son kare mata
Mashawarcin shugaba Tinubu kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana muhimmancin kare mata daga yin amfani da su wajen safarar makamai.
Ya kara da cewa mata na da muhimmanci wajen samar da zaman lafiya, saboda haka ya dace a kare su daga illolin rashin tsaro.
An kama mata masu safarar makamai
A baya mun ruwaito cewa jami'an tsaron kasar nan sun yi nasarar dakume wata mata mai suna Aisha Abubakar da harsasai da ta ke kokarin kai wa ga 'yan ta'adda a jihar Katsina.
Jami'an tsaro sun kama matar da alburusan, amma ta ki amsa cewa na ta ne, sai bayan an matsa da bincike ne ta bayyana cewa ta dauko kullin daga Kaduna za ta kai su karamar hukumar Dan Musa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng