An yi Mummunan Haɗari a Ranar Maulidi, Mutane Kusan 20 Sun Kone Kurmus

An yi Mummunan Haɗari a Ranar Maulidi, Mutane Kusan 20 Sun Kone Kurmus

  • Yayin da al'ummar Musulmi ke jerin gwanon bikin Maulidi a Najeriya an samu haɗarin mota a titin Ijebu-Ode zuwa Benin
  • An ruwaito cewa mutane 18 ne suka kone kurmus bayan wuta ta tashi a motar da ta yi hadarin, wasu da dama kuma sun jikkata
  • An ruwaito cewa man fetur ne da aka ajiye a cikin motar ya jawo ta kama da wuta bayan motar ta wantsila ta baya baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - An samu mummunan haɗarin mota a kan hanyar Ijebu-Ode zuwa Benin a ranar Litinin da ta wuce.

Rahotanni sun nuna cewa da yawa daga cikin mutanen da ke cikin motar sun mutu ta hanyar konewa kurmus.

Kara karanta wannan

An koma makoki bayan mutuwar ƴan Maulidi 36 a hatsarin mota, wasu 31 na asibiti

Jihar Ogun
Mutane 18 sun mutu a hadarin mota a Ogun. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'in TRACE mai lura da wucewar abubuwan hawa, Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane 18 sun kone yayin hadari

Jami'in TRACE mai lura da zirga zirgar abubuwan hawa a Ogun ya tabbatar da cewa mutane 18 sun rasu yayin hadarin mota a titin Ijebu-Ode zuwa Benin.

Babatunde Akinbiyi ya ce mummunan hadarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 03:30 na yamma.

Yadda mutane suka kone a hadarin mota

Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da cewa motar ta bugi wani sashe na hanya ne alhali akwai gora da aka ajiye fetur a ciki kuma daga nan sai wuta ta tashi.

The Cable ta wallafa cewa bayan wutar ta tashi mutane 18 a cikin motar suka kone kurmus kuma an kai gawarsu babban asibitin Ijebu-Ode.

Matukin mota ya tsallake rijiya ta baya

Kara karanta wannan

Seaman Abbas: Muhimman abubuwa 7 a labarin sojan ruwan da ya ja hankalin ƴan Najeriya

Sai dai rahotanni sun nuna cewa matukin motar ba ya cikin wadanda suka kone yayin haɗarin.

Sai dai duk da haka, Babatunde Akinbiyi ya ce matukin motar ya samu munanan raunuka kuma yana asibiti yana karɓar magani.

Hadarin Maulidi: Gwamna ya yi jaje

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kaduna ta mika ta'aziyya ga iyalan mutum 40 da su ka rasu a hanyar Saminaka a hadari.

Mutanen sun rasu ne a hanyarsu ta zuwa Maulidi, yayin da akalla mutum 48 da su ka tsira da rai, su ke asibiti su na karbar magani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng