Ambaliya: Dattijon Attajiri, Dantata Ya Tallafawa Borno da Sama da Naira Biliyan 1

Ambaliya: Dattijon Attajiri, Dantata Ya Tallafawa Borno da Sama da Naira Biliyan 1

  • Gwamnatin Borno ta kara samun tallafi domin a hada karfi da karfe wajen tallafa wa mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri
  • A wannan jikon, Attajirin Dattijo, Alhaji Aminu Dantata ne ya bayar da tallafin Naira Biliyan 1.5 domin a tallafa wa jama'ar garin
  • Mummunar ambaliyar da aka gamu da ita ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane, yayin da ta shafi kusan mutane miliyan biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Attajiri, Alhaji Aminu Dantata ya ziyarci jihar Borno domin jajanta wa gwamnati da al'uma bisa iftila'in ambaliya.

Mutane sama da miliyan biyu ambaliyar ta shafa, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da bayar da agaji bayan rasuwar akalla mutum 37.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Shugaba Tinubu zai nema wa jama'a taimako, ya kafa asusun tallafi

Borno
Alhaji Aminu Dantata tallafa wa gwamnatin Borno da N1.5bn Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa dattijon attajirin ya jagoranci tawagar ta'aziyya da nuna alhini a ranar Talatar nan zuwa gidan gwamnatin jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya: Alhaji Dantata ya ba da tallafin N1.5bn

Jaridar aminiya ta wallafa cewa shahararren dan kasuwa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya ba jihar Borno tallafin Naira Biliyan 1.5.

Ya kuma mika ta'aziyya ga gwamna Babagana Umara Zulum da sauran jama'ar Borno, musamman wadanda iftila'in ya shafa.

Dantata ya gargadi shugabanni bayan ambaliya

Alhaji Aminu Dantata ya gargadi shugabanni da su ji tsoron Allah domin halin da jama'a ke ciki akwai kunci da talauci a yanzu.

A martaninsa, gwamnan Borno, Babagana Zulum ya gode wa dattijon dan kasuwar, tare da bayyana cewa tallafinsa zai taimaka wa jama'ar Maiduguri kwarai da gaske.

Ambaliya: Tinubu na nemawa Maiduguri tallafi

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ba da tallafin N100m ga wadanda ambaliya ta shafa a Maiduguri

A wani labarin kuma, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana samar da asusun tallafi domin mutanen da ambaliya ta shafa a jihar Borno jim kadan bayan ya dawo kasar nan.

Shugaban ya bayyana haka ne a ziyarar jaje da duba halin da mutanen Maiduguri ke ciki bayan mummunar ambaliya irinta ta farko a cikin shekaru 30 a jihar Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.